Mutuwar daliba: Gwamnatin Katsina ta dauki mataki a kan shugaban makaranta da malami

Mutuwar daliba: Gwamnatin Katsina ta dauki mataki a kan shugaban makaranta da malami

Gwamnatin jahar Katsina ta Gwamna Aminu Bello Masari ta sanar da dakatar da shugabar makarantar gwamnati ta larabci ta yan mata dake garin Fago a garin Daura, Fatima Yakubu biyo bayan mutuwar wata dalibar kwalejin, Fatima Maikano.

Daily Trust ta ruwaito gwamnatin ta dakatar da Fatima Yakubu ne saboda nuna halin ko in kula da ta yi game da mutuwar dalibar, haka zalika gwamnati ta sallami malamin da ya zane Fatima Maikano, Abubakar Sulaiman, daga aiki gaba daya.

KU KARANTA: Kowa da matsalarsa: Matashi ya kama hanya a kasa don jinjina ma Sarkin Kano Aminu daga Jigawa

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Abubakar yana koyar da darasin lissafi ne a makarantar a matsayin wucin gadi, inda ya zane Fatima Maikano, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarta.

Kwamishinan ilimi na jahar Katsina, Badamasi Lawal ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Talata bayan kammala taro da iyayen mamaciyar, inda yace an kafa kwamiti don bincikar lamarin.

Kwamishinan ya kara da cewa daga yanzu gwamnan jahar Katsina ya haramta duk wani nau’o’in ladabtarwa na gwale gwale a makarantun jahar Katsina, sa’annan an haramta ma malamai dukan dalibai da bulala kowanne iri, don haka ya nemi shuwagabannin makarantu su lura.

A nasa jawabin, mahaifin Fatima Maikano, Tasiu Maikano ya bayyana cewa matakin da ma’aikatar ilimi ta dauka zai rage musu radadin mutuwar diyarsu.

Idan za’a tuna bayan Malam Abubakar ya zane Fatima Maikano ne saboda bata bayar da wani aikin gida da ya basu ba ne sai ta fara rashin lafiya, kuma bata samu kulawar makarantar ba, har sai da iyayenta suka isa makarantar don ganin da take ciki, daga nan ta rasu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel