Sunusi ya baiwa Ganduje sa’o’i 24 ya sake shi, ko kuma ya dauki mataki a kansa

Sunusi ya baiwa Ganduje sa’o’i 24 ya sake shi, ko kuma ya dauki mataki a kansa

Korarren sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II ya dauki alwashin shigar da gwamnatin jahar Kano gaban kotu biyo bayan tsige shi da ya yi daga mukamin Sarautar Kano, tare da garkame shi.

Lauyan Sanusi, Abubakar Mahmoud SAN ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Talata, inda yace Sunusi ya basu umarnin kalubalantar tsige shi da aka yi, da kuma garkame shi da aka yi.

KU KARANTA: An garzaya da tsohon sarkin Kano zuwa sabon gidan da zai zauna a Awe

A cewar Mahmoud, garkame Sarki a wani wuri tare da hana shi walwala ba shi da asali a kundin tsarin mulkin Najeriya, don haka ya yi kira ga gwamnatin Kano ta sakan masa mara ya yi fitsari cikin sa’o’I 24 ko kuma ya kai shi kotu.

“Sakamakon umarnin tsohon Sarki ta hannun babban hadiminsa, ya bamu daman shigar da karar gwamnati gaban kotu domin kalubalantar tsige garkame shi tare da fatattakarsa daga garin Kano, muna da tabbacin hakan ya saba ma sashi na 35 na kundin tsarin mulkin Najeriya daya baiwa kowa daman walwala.

“Mun sanar da kwamshinan Yansanda haramcin takura ma Sarki tare da garkame shi da kuma hana shi walwala, hatta kais hi jahar Nassarawa ba tare da son ran shi ba, Sarkin ya shaida ma kwamishinan Yansanda cewa abokansa sun shirya masa jirgi da zai dauke shi tare da iyalansa zuwa Legas, don haka ya nemi a basu tsaro har zuwa filin sauka da tashin jirage don su yi tafiyarsu.

“Amma kwamshinan ya ki, saboda a cewarsa wannan ba shi bane umarnin da aka bashi, kwamishinan yace sun yarda iyalan Sarkin su tafi Legas, amma Sarki ya bi su su tafi Abuja, daga nan su kai shi Nassarawa. Ta tabbata jami’an tsaro a shirye suke su tilast Sarkin, don haka muka biye musu.

“Mun raka gwamnan har zuwa sansanin rundunar Sojan sama dake Kano inda aka dauki Sarkin a wani jirgi da misalin karfe 6:40 na dare, daga nan iyalansa kuma suka bi jirgin da abokansa suka shirya masa suka tafi Legas.

“Wannan dokar sallamar sarki mai murabus daga gari ya samo asali ne a zamanin mulkin turawa na mulkin mallaka, amma ba shi da tushe a kundin tsarin mulkin Najeriya. Don haka muka yi mamakin yadda hakan ya cigaba da aiki a wannan zamani.” Inji shi.

Daga karshe Mahmoud ya yi kira ga yan Najeriya da kasashen duniya su sa baki don tabbatar da an saki Muhammadu Sunusi don kare raywarsa da tabbatar da yancinsa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel