Tsohon sarki Sanusi II ya garzaya Kotu
Tsohon Sarkin Kano da aka sauke daga kan kujerarsa a ranar Litinin, Sanusi Lamido, ya lashi takobin bin hakkinsa a kotu domin kalubalantar tsige shi da kuma kange shi a wani wuri da sunan gudun hijira.
Lauyan sarki Sanusi, Abubakar Mahmoud (SAN), ne ya bayyana hakan da yammacin yau, Talata, yayin gana wa da manema labarai a Abuja.
Lauyan ya ce sauke Sanusi da tsare shi a wata mafaka sun saba wa doka tare da take hakkinsa na bil'adama.
A ranar Litinin ne gwamnatin Kano, ta bakin Usman Alhaji, sakataren gwamnatin jiha, ta sanar da sauke Sanusi II daga kujerar sarkin Kano bisa zarginsa da rashin biyayya ga sabbin dokokin masarautun jihar Kano da aka kirkira a karshen shekarar 2019.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng