Sheikh Ahmad Gumi ya yi 'ragargaza' a kan tsige Sanusi II

Sheikh Ahmad Gumi ya yi 'ragargaza' a kan tsige Sanusi II

Babban malamin addinin Islama da ke zaune garin Kaduna, Sheikh Ahmed Gumi, ya bayyana cewa tsarin sarautar gargajiya ya gama lalacewa, a saboda haka bashi da wani sauran tasiri a Najeriya.

Sheikh Gumi ya bayyana hakan ne yayin da ya ke tofa albarkacin bakinsa a kan tube rawanin Sanusi II da gwamnatin jihar Kano ta yi a ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairu.

A ranar Litinin ne gwamnatin Kano, ta bakin Usman Alhaji, sakataren gwamnatin jiha, ta sanar da sauke Sanusi II daga kujerar sarkin Kano bisa zarginsa da rashin biyayya ga sabbin dokokin masarautun jihar Kano da aka kirkira a karshen shekarar 2019.

A martaninsa a kan sauke Sanusi, wanda ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta, Sheikh Gumi ya bayyana cewa, "tsarin sarautar gargajiya abu ne mai kima da daraja a duniyar da, amma yanzu, abin takaici, bashi da wani tasiri saboda addini da kuma nada wadanda basu cancanta ba."

Fitaccen mamalin addinin ya bayyana cewa tsarin mulkin sarauta ya ci karo da koyarwar addinin Islama tare da fadin cewa "addinin Islam bai yarda a yi wa wani mutum 'gurfane' ba sai Allah shi kadai".

Sheikh Ahmad Gumi ya yi 'ragargaza' a kan tsige Sanusi II
Sheikh Ahmed Gumi
Asali: Depositphotos

"Addinin Musulunci bai yarda da tsarin samun mulki ta hanyar gado ba, sai dai ta hanyar maslaha (shurah) da amincewar jama'a. Asalin mazhabar Shi'a ta samo asali ne daga kafewa a kan samun mulki ta hanyar gado

"Makasudin Jihadin Sokoto shine tabbatar da biyayya ga tsarin addini da adalci da zasu yi daidai da koyarwar Islama.

DUBA WANNAN: Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)

"Ba zai yiwu wani mutum ya kira kansa mai kare Islam da al'adu ba amma kuma ya kasance daga cikin masu assasa danniya da rashin adalci ga bil'adama ba. Wannan kuma shine hali mai muni da sarautar gargajiya ta yau ta ginu a kai

"Mutum zai iya kasancewa mai mugunta kuma Allah ya kyale shi, amma duk wanda ya buya a inuwar addini domin kulla makirci da rashin gaskiya, asirin shi zai tonu cikin gaggawa.

"Wannan shine dalilin da yasa Allah, cikin hikimarsa, ya wulakanta tsarin mulkin sarautar gargajiya. Abu mafi alkhairi shine a rushe tsarin baki dayansa."

Babban malamin ya buka jinin su sarauta su kasance kamar sauran mutane tare da zama masu biyayya ga doka kamar sauran 'yan kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel