Tsige Sanusi: 'Ba ni na kar zomon ba'; Fatima Ganduje ta yi wa masu sukarta martani

Tsige Sanusi: 'Ba ni na kar zomon ba'; Fatima Ganduje ta yi wa masu sukarta martani

- Diyar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, Fatima Ajimobi, ta bukaci mutane da su daina saka ta cikin lamarin da ya faru a jiya Litinin

- Hakan ya biyo bayan zagi da cin zarafi da take fuskanta daga jama'a a kafafen sada zumuntar zamani

- Fatima dai daya daga cikin 'yayan gwamnan jihar Kano din ce wacce ke auren dan tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi

Diyar gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, Fatima Ajimobi ta bukaci mutane da su daina saka ta cikin lamarin da ya faru a jiya Litinin na tsige sarki Sanusi daga karagar mulkin jihar Kano.

Hakan ya biyo bayan zagi da cin zarafi da take fuskanta daga jama'a a kafafen sada zumuntar zamani. Ta bukaci mutane da su daina kiran sunanta tare da jawo hankalinta a duk lokacin da zasu yi maganar lamarin.

A ranar Litinin, 9 ga watan Maris ne Gwamnan Ganduje ya tsige Muhammadu Sanusi II daga karagar mulkin jihar Kano. Wannan lamarin kuwa ya matukar girgiza 'yan Najeriya. A take kuwa suka fara cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani a kan tsige sarkin.

Tsige Sanusi: 'Ba ni na kar zomon ba'; Fatima Ganduje ta yi wa masu sukarta martani

Tsige Sanusi: 'Ba ni na kar zomon ba'; Fatima Ganduje ta yi wa masu sukarta martani
Source: Facebook

DUBA WANNAN: Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)

Fatima dai daya daga ckin 'yayan gwamnan jihar Kano din ce wacce ke auren dan tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi.

Wasu daga cikin ma'abota amfani da kafar sada zumuntar zamani sun dinga zagin gwamna Ganduje tare da kiran sunan Fatima Ajimobi a wallafar ta yadda hankalinta zai kai.

A take kuwa ta wallafa cewa a daina kiran sunanta don ba ita ta kashe zomon ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel