Matasan Arewa sun ba Shugaba Buhari da manyan kasa laifi kan tsige Sanusi II

Matasan Arewa sun ba Shugaba Buhari da manyan kasa laifi kan tsige Sanusi II

Shugaban kungiyar Arewa Youth Organizations ta Matasan Arewacin Najeriya, Murtala Abubakar, ya yi magana game da tsige Sarki da gwamnati ta yi a kasar Kano.

Mista Murtala Abubakar ya bayyana cewa akwai laifin shugaba Muhammadu Buhari wajen wannan mataki da gwamnatin jihar Kano ta dauka na tunbuke Sarkin Birni.

Jaridar Vanguard ta ce wannan kungiya ta zargi Dattawan Arewacin Najeriya da cewa ba su yi kokarin ganin sun shiga tsakanin tsohon Sarki da gwamnan Jihar Kano ba.

An dauki tsawon lokaci ana samun matsala tsakanin tsohon Mai Martaba watau Malam Muhammadu Sanusi II da kuma Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A na sa bangaren shugaban kasa Muhammadu Buhari bai ce komai ba kusan duk tsawon wannan rikici da aka yi wanda akalla an shafe shekaru biyu ba a samun jituwa.

KU KARANTA: Muhammadu Sanusi II zai iya komawa kan kujerar sa - Lauyansa

Matasan Arewa sun ba Shugaba Buhari da manyan kasa laifi kan tsige Sanusi II

Yunkurin Manyan Arewa na sasanata Gwamnatin Kano da Sanusi II bai yi aiki ba
Source: UGC

“Da ace shugabannin Arewa sun sa baki da tuni an manta da kawo karshen rikicin da ya ki ci - ya ki cinyewa tsakanin Muhammadu Sanusi II da aka tunbuke da kuma gwamna.”

Shugaban wannan kungiya ta Matasa ya jefi manyan yankin na Arewa da kin nuna kishin al’umma. A cewar Abubakar, wannan shirun na manya bai taimakawa Yankin ba.

Kungiyar ta bakin Murtala Abubakar ta ce: “A matsayinmu na shugabannin Matasa, za mu rike shugaban kasa Muhammadu Buhari da laifi idan har rikici ya barke a cikin Kano.”

Wannan kungiya ta fito ta na cewa danyen aiki da gwamnati ta yi, ya na iya jawo tashin hankali. Haka zalika kungiyar ta ce shiru-shirun Buhari ta sa Ganduje ya tsige Sarkin.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel