Solomon Dalung: Gwamnatin APC ba ta cika alkawaran da ta yi kamar yadda jama’a za su so ba

Solomon Dalung: Gwamnatin APC ba ta cika alkawaran da ta yi kamar yadda jama’a za su so ba

Tsohon Ministan wasannin Najeriya, Salomon Dalung ya zanta da Jaridar BBC Hausa inda ya yi magana game da yadda kasar ta ke tafiya a karkashin gwamnatin APC.

Solomon Dalung ya nuna cewa bai ji haushi saboda kin maidasa kujerar Ministan wasannin Najeriya a wannan wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari na biyu ba.

Dalung ya ce: “Jama’a ba za su fahimci dangataka da shugaba Buhari ba, ba a nan ta ke ba. Na dauki lokaci mu na tare da Buhari. Tun ya na gwagwarmaya mu ke tare.”

“Tun lokacin har yau mu na tare da Buhari. Na yi gwagwarmaya domin a zabe shi ne ba don neman abin Duniya ba. Sai dai don kasa za ta samu cigaba a mulkinsa.”

“Saboda haka a gare ni, rashin komawa ta Minista, ba abu ne wanda ya dame ni ba. Sai dai ina godewa Allah, da abin sharrin da ya kare ni da shi a sakamakon haka.”

KU KARANTA: Wasu Gwamnoni za su nemi ganawa da Buhari kan rikicin APC

Ba mu cika alkawaran da mu ka yi kamar yadda jama’a za su so ba – Dalung
Ba neman abin Duniya ta sa na ke bin Shugaba Buhari ba – Solomon Dalung
Asali: UGC

A cewar tsohon Ministar, watakila akwai alheri a hanin da ya samu wannan karo. Game da alkawuran da APC ta yi wa al’umma, Dalung ya ce ba a kai ga cika su ba.

Duk da Solomon Dalung ya tabbatar da cewa akwai sauran aiki a gaban gwamnatin Buhari, ya nuna cewa ya na sa rai akwai lokacin da za a cika wadannan alkawari.

“Ba mu samu biyan bukata kamar yadda ‘Yan Najeriya su ka so ba. Amma ba mu fitar da imani cewa za mu iya saukar da wadannan nauyi kafin Buhari ya sauka ba.”

Mista Dalung ya kara da cewa akwai matsala idan har wannan gwamnati mai-ci ta gaza sauke alkawauran da ta dauka a lokacin da ta ke yakin neman zaben kasar a 2015.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel