Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)

Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)

A ranar Litinin ne kafofin yada labarai da na sada zumuntar zamani suka rincabe da zancen tube rawanin Malam Muhammadu Sanusi II, sarkin Kano kashi na 14.

Bayan tube rawaninsa da gwamnatin jihar Kano, karkashin jagorancin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tayi, tuni jami'an tsaro suka mamaye harabar fadar sarkin Kano din.

Babu jimawa suka fitar dashi sannan aka nuf jihar Nasarawa da tsohon Sarkin. Ana tsammanin tubabben sarkin zai kare rayuwarsa ne a kauyen Loko da ke karamar hukumar Nasarawa da ke jihar Nasarawan Najeriya.

Ga hotunan gidan da zai zauna a jihar:

Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)
Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)
Asali: Twitter

Bayan aukuwar lamarin, kungiyar dattijan Kano karkashin shugabanci Bashir Tofa sun yi Alla-wadai da lamarin.

Sun bayyana cewa komai kaddara ce kuma zasu ci gaba da karbar kaddarar Ubangiji. Amma tabbas lamarin ya matukar gigitasu da basu tsananin mamaki.

Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)
Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)
Asali: Twitter

Daga nan ne suka yi kira ga jama'ar Kano a kan su kwanatar da hankulansu tare da gujewa kowacce husuma ko tasin-tashina don kalubalantar lamarin.

Kungiyara dattajina ta tabbatar da cewa ba za ta yi kasa a guiwa ba, sai ta garzaya gaban kotu don kalubantar lamarin ta halastacciyar hanya.

Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)
Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Tube rawanin Sanusi: Dattijan Kano sun yi wa Ganduje zazzafan martani

Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)
Inda ake tsammanin tsohon sarki Sanusi zai kare rayuwarsa (Hotuna)
Asali: Twitter

A takardar da shugaban majalisar dattijan Kano, Bashir Usman Tofa yasa hannu, ya kwatanta tube rawanin Sarkin da abin takaici kuma wanda aka yi ba tare da bin ka’ida ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel