Farfesa Osinbajo ya na taimakawa Gwamnatinmu Inji Shugaban kasa Buhari

Farfesa Osinbajo ya na taimakawa Gwamnatinmu Inji Shugaban kasa Buhari

A Ranar Lahadi, 8 ga Watan Maris, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito ya bayyana irin amfanin mataimakinsa, Farfesa Yemi Osinbajo, a tafiyar wannan gwamnati.

Shugaba Muhammadu Buhari ya ke cewa mataimakin na sa ya taimaki gwamnatin da ya ke jagoranta. A zaben 2015 aka zabi shugaban kasar da mataimakinsa a Najeriya.

Shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya kira Mai girma Yemi Osinbajo wayar salula domin taya sa murnar zagayowar ranar haihuwarsa a jiya Ranar Lahadi.

Rahotanni daga fadar kasar sun ce Buhari ya na yabawa Osinbajo, da cewa ya taka rawar gani a tsare-tsaren tattalin arziki da wasu shirye-shirye da gwamnatin APC ta kawo.

Buhari ya ke cewa mataimakin na sa ya bada gudumuwa sosai ga manufofin wannan gwamnati na kawo hanyoyin rage radadin talauci da fitar da ‘Yan Najeriya daga cikin kunci.

KU KARANTA: Osinbajo: Tinubu ya yaba da irin halin Mataimakin Shugaba Buhari

Farfesa Osinbajo ya na taimakawa Gwamnatinmu Inji Shugaban kasa Buhari
Buhari ya yi wa Farfesa Osinbajo karin lafiya da tsawon kwana
Asali: Depositphotos

Haka zalika shugaban kasar ya yabawa mataimakinsa Osinbajo a game da jajircewarsa tukuru wajen aiki da kuma nuna amana ga Mai gidan na sa watau Muhammadu Buhari.

Shugaban Najeriyar ya yi wannan jawabi ne ta bakin Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu. Shehu ya fitar da wannan jawabi ne jiya yayin taya Osinbajo murna.

A jiya ne manyan kasar nan su ka rika fadan abin kirki game da mataimakin shugaban na Najeriya. Daga ciki har da tsohon Mai gidansa, Bola Tinubu da Hadiminsa Laolu Akande.

Yayin da Farfesa Osinbajo ya ke cika shekaru 63 a ban kasa, har wasu ‘Yan siyasa da ke karkashin jam’iyyar PDP sun ajiye banbancin siyasa sun yi wa shugaban addu’a ta gari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel