Yarinya yar shekara 16 ta kashe abokin mahaifinta da ya yi kokarin lalata da ita

Yarinya yar shekara 16 ta kashe abokin mahaifinta da ya yi kokarin lalata da ita

Jami’an rundunar binciken manyan laifuka na rundunar Yansandan Najeriya,SCIID, sun kaddmar da bincike kan dalilin da ya sabbaba mutuwar wani mutumi dan shekara 49 mai suna Babatunde Ishola.

Ana zargin wata daliba yar shekara 16 mai suna Timilehin Taiwo, diyar abokinsa ne ta kashe shi a lokacin da ya yi kokarin haike mata da nufin yin lalata da ita ta hanyar fyade, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

KU KARANTA: Majalisar dokokin jahar Kaduna ta yi dokar rage talauci a tsakanin talakawan Kaduna

Lamarin ya faru ne a gida mai lamba 10 dake titin Ogundele a unguwar Aboru na jahar Legas, kuma DPO na Yansandan yankin, Oke Odo, ya ziyarci wurin da kansa, inda ya tarar da gawar mamacin kwance cikin jini.

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Legas, Bala Elkana ya bayyana cewa: “An dauke gawar mamacin zuwa asibiti domin a gudanar da bincike a kan gawar, an kama wanda ake zargi, kuma an amshe wukar da ta kashe shi da shi.

“A jawabinta, yarinyar ta bayyana cewa mamacin wanda abokin mahafinta ne ya gayyace ta zuwa gidansa don ta taya shi diban ruwa saboda shi kadai yake zama ba shi da mata a gidan, ta ce ta dade tana taimakonsa da yi masa aikace aikacen gida.

“Amma yayin da take debo masa ruwa a ranar Asabar sai ya yi kokarin haike mara, a nan ne ta dauki wuka ta caka masa, an mika yarinyar zuwa asibiti domin tabbatar da matsayin hankalinta, kuma kwamishinan Yansandan jahar Legas, Hakeem Odumosu ya bada umarnin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.” Inji shi.

A wani labarin kuma, dan kwallon Najeriya, Chineme Martins dake tsaron gida a kungiyar kwallon kafa ta Nassarawa United ya yanke jiki ya fadi, daga nan ya sheka barzahu a yayin da yake tsaka da taka leda.

Dan kwallon ya gamu da ajalinsa ne a lokacin da kungiyarsa ta Nassarawa United ke karawa da kungiyar Katsina United, a filin wasa na Lafia dake jahar Nassarawa a ranar Lahadi, 8 ga watan Maris.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel