Kasar Afrika ta Kudu ta nada Ngozi Okonjo-Iweala cikin Majalisar tattalin arziki

Kasar Afrika ta Kudu ta nada Ngozi Okonjo-Iweala cikin Majalisar tattalin arziki

Ganin halin da tattalin kasar Afrika ta Kudu ta shiga, shugaba Cyril Ramaphosa ya fadada babban majalisar tattalin arzikinsa domin a shawo kan wannan matsala.

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta na cikin wadanda aka sa a cikin wannan majalisa mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tattalin arziki domin fitar da kasar daga kangi.

Shugaba Cyril Ramaphosa wanda ya hau mulki a 2018 ya dauki wannan mataki ne bayan tattalin arzikin kasarsa ya durkushe har sau biyu a cikin ‘yan shekarun bayan nan.

A taron da majalisar ta yi a karshen makon jiya, an bada sanarwar cewa an sa tsohuwar Ministar tattalin Najeriya cikin wannan majalisa domin ta bada irin gudumuwarta.

Shugaba Ramaphosa ya kaddamar da uwar wannan majalisa ne a karshen shekarar bara. Shugaban kasar ya bukaci majalisar ta rika kawowa gwamnati dabarun tattali.

KU KARANTA: Takaitaccen tarihin Ministan tsaron Najeriya na farko

Kasar Afrika ta Kudu ta nada Ngozi Okonjo-Iweala cikin Majalisar tattalin arziki
Dr. Ngozi Okonjo-Iweala tare da Shugaban kasar Afrika ta Kudu
Asali: UGC

Wannan majalisa ta na zaman gashin kanta ne, kuma ta na da cikakken ‘yanci. An zakulo ‘ya 'yan ta ne daga kwararrun ‘Yan Boko da ‘Yan kasuwa da Masanan da ake ji da su.

Shugaban kasar ta Afrika ta Kudu shi ne ke jagorantar wannan majalisa da za ta yi aikin shekaru uku. Za a rika biyan ‘yan majalisar kudin mota da kudin lokacinsu da aka mora.

‘Yan wannan majalisa za su rika bada shawarwari a kan harkar tattaki, kasuwanci, kwadago, samar da aikin yi, talauci, cigaban birane, sha’anin kafa kamfanoni da sauransu.

Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta shafinta na Tuwita ta tabbatar da cewa har ta zauna da shugaban kasar da kuma majalisar ta sa domin taimakon kasar da kuma daukacin Yankin Afrika.

Idan ba ku manta ba, Dr. Ngozi Okonjo-Iweala ta rike Ministar kudi sau biyu a Najeriya, sannan ta yi aiki a babban bankin Duniya, ta na cikin Matan da ake ji da su a Nahiyar nan.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng