Takaitaccen tarihin kakan Aisha Buhari: Ministan tsaro ma farko a Najeriya
Aisha Buhari ta fito ne daga babban gida na 'yan Boko da suka rike manyan mukamai a gwamnatin Najeriya.
Muhammadu Ribadu, kakan Aisha Buhari, fitaccen dan siyasa ne a yankin arewa da ma Najeriya baki daya.
An nada Muhammadu Ribadu a matsayin ministan tsaro na farko na kasa bayan samun 'yancin kai. An nada shi a matsayin mamba a majalisar kasa a shekarar 1947 kafin daga bisani a sake zabensa a shekarar 1951.
Ya taba zama mamba a hukumar raya harkokin noma ta Najeriya kafin daga baya ya zama mamba a bangaren bayar da rance a hukumar cigaban yankin arewa.

Asali: Twitter
An zabe shi a matsayin wakili a taron sake yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima a garin Ibadan a shekarar 1950.
DUBA WANNAN: Fansho da albashi: SERAP ta fitar da sunayen tsofin gwamnoni da ke cin 'tudu biyu' a asusun Najeriya
A shekarar 1952 ne aka nada shi a matsayin ministan albarkatun kasa. An zabe shi a mata mataimakin shugaban jam'iyyar NPC, mukamin da yasa ake saka shi a cikin jerin manyan shugabannin da suka fito daga arewa irinsu Ahmadu Bello da Tafawa Balewa.
Ya rike mukamin ministan kasa, ma'adanai da lantarki a shekarar 1954, ya zama ministan kasa da harkokin Lagos a shekarar 1959.
An haife shi a shekarar 1910, ya mutu a shekarar 1965, watau yana da shekara 55 a duniya.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng