Fastoci: ‘Yan Sanda sun yi ram da Matar da ta ke yaudarar Bayin Allah a coci

Fastoci: ‘Yan Sanda sun yi ram da Matar da ta ke yaudarar Bayin Allah a coci

Wata Baiwar Allah mai suna Bose Olasunkanmi, ta shiga hannun Jami’an tsaro, a sakamakon amfani da ita da Fastocin Najeriya su ke yi wajen damfarar Mabiyansu.

Kamar yadda mu ka samu labari, Fastoci da-dama sun saba aiki da wannan Mata wajen kokarin nuna baiwar bogi da kuma mu’ijizar karya da su ke ikirarin su na da su.

A halin yanzu Dakarun IRT na Yankin Legas da ke karkashin ofishin Sufeta Janar na ‘Yan Sanda, sun kama wannan Mata bayan tsawon watanni ana dakonta a Najeriya.

Tun a Oktoban 2019, sunan Madam Olasunkanmi ya fara yawo inda bidiyoyinta su ka rika karada kafofin sadarwa, da sunan cewa an warkar da ciwon da ke hannunta.

Bose Olasunkanmi ta na da tawaya a hannunta wanda ta maida hanyar samun kudi. A karshe dai ta amsa laifinta da kanta, inda ta bayyana cewa damfarar jama’a ta ke yi.

KU KARANTA: Wata Mata ta ce za ta ba Mijinta damar sheke aya a waje

Fastoci: ‘Yan Sanda sun yi ram da Matar da ta ke yaudarar Bayin Allah a coci

Jami'an ‘Yan Sanda sun kama Olasunkanmi mai yaudarar mutane a coci
Source: UGC

Kamar yadda mu ka samu labari, Bose Olasunkanmi, ta hadu ne da wata Mata mai suna Misis Fatila Musa, wanda ta nuna mata hanyar samun kudi wajen nuna mu’ijizar karya.

Tun daga nan wannan mata ta koma kawowa Fastoci marasa lafiyan karya, wadanda ake yaudarar Mabiya Kirista da sunan cewa an yi masu magani har sun samu waraka.

Wannan Mata ta ke cewa da kanta: “Duk inda ku ka gan ni a cikin bidiyo a wani coci, babu Malamin da ya warkar da ni. Gayyatata ake yi, ni kuma in yi lambo kamar na warke”

Wannan Mata da aka saba amfani da ita wajen yaudarar Jama’a a wajen bauta ta zagaya coci a Jihohi irinsu Legas, Ribas, Ebonyi da wasu Garuruwa ta na yin wannan danyen aiki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel