NDLEA ta kama Madam Queen, babbar dilar miyagun kwayoyi a Sokoto da aka dade ana nema ruwa a jallo
Bayan an kai ruwa rana, jami'an hukumar hana sha da safarar miyagun kwayoyi (NDLEA) ta samu nasarar cafke babbar dilar miyagun kwayoyi, Madam Queen, tare da wasu mutane 18 yayin wani ofireshon a Sokoto.
Madam Queen, shahararriyar dilar miyagun kwayoyi, ta dade a cikin jerin mutanen da hukumar NDLEA ke nema ruwa a jallo a jihar Sokoto.
Da yake gana wa da manema labarai jim kadan bayan kama masu laifin a karshen mako, kwamandan NDLEA a jihar Sokoto, Mista Yakubu Kido, ya bayyana cewa hukuma ta shafe fiye da shekaru 10 tana neman Madam Queen.
A cewar Kido, mai lafin ta dade tana kasuwancin saye da safarar miyagun kwayoyi da tabar wiwi a fadin jihar Sokoto kafin daga bisani a samu nasarar kama ta tare da wasu yaranta 18 da ke taya ta sayar da miyagun kwayoyi.
Kwamanda Kido ya bayyana cewa Madam Queen tana zaune ne a kauyen Raymond da ke karkashin karamar hukumar Dange Shuni kafin jami'an NDLEA su kama ta a ranar 28 ga watan Fabrairu.
DUBA WANNAN: Jami'an FRSC sun fasa tayar motar matar da ta dauko mai nakuda (Bidiyo)
Kazalika, Kido ya sanar da cewa an samu miyagun kwayoyi da suka hada da allurar 'Pentazocine' a tare da ita.
"Allurar 'Pentazocine' tana cikin rukunin 'A' na haramtattun miyagun kwayoyi a duk fadin duniya," a cewar Kido.
Da yake karin bayani, Kido ya bayyana cewa ofishin NDLEA reshen jihar Sokoto ya kama miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai 141.53kg a cikin watan Fabrairu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng