Shehu Sani ya roka wa Sarki Sanusi gafara a wajen Ganduje

Shehu Sani ya roka wa Sarki Sanusi gafara a wajen Ganduje

Tsohon dan majalisar dattijai, Sanata Shehu Sani ya roki Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano a kan ya yafe wa Sarkin Kano, Malam Muhammadu Sanusi II a kan duk wani abinda ya yi ba dai-dai ba.

Sani ya sanar da hakan ne a yau Juma’a a wallafa da yayi a shafinsa na Twitter. Ya yi kira ga Gwamna Ganduje a kan “ya yi yafiya, ya kuma manta da abinda ya wuce ya kyale sarki Sanusi II”.

Ya kara da kira ga gwamnan da ya sani cewa mulki na juyi ne kuma watarana zai iya bukatar taimakon Sarkin.

Sarkin Kano din dai na fuskantar sabuwar tuhuma ne daga hukumar sauraron koke da yaki da rashawa ta jihar Kano, a kan zargin damfarar naira biliyan 2.2 na fili.

Shehu Sani ya roka wa Sarki Sanusi gafara a wajen Ganduje
Shehu Sani ya roka wa Sarki Sanusi gafara a wajen Ganduje
Asali: Twitter

Sarkin mai matsayi na farko zai bayyana a gaban kungiyar masu bincike ne ta hukumar a jiya amma sai bai samu zuwa ba. Ya bukaci a saka masa wata rana daban don zuwa amsa tambayoyinsu.

Amma kuma a yau Juma’a ne hukumar ta jaddada cewa tilas ne sarkin ya bayyana gabanta don amsa tambayoyinta a ranar 9 ga watan Maris din 2020.

DUBA WANNAN: Za a fara biyan 'yan N-Power allawus din Janairu da Fabrairu ranar Juma'a - FG

Sanannen abu ne idan aka ce akwai Baraka tsakanin gwamnan da Sarki Sanusi kuma hakan yasa aka fara masa sabuwar tuhumar bayan ta farko din da ta tarwatse a kotu.

Ba wannan bane karon farko da masarautar Kano din ake bincikarta tun bayan da Malam Muhammadu Sanusi II ya hau karagar mulkinta a 2014.

Hukumar binciken ta binciki Sarki Sanusi a kan abinda ta kwatanta da kisan kudi ba bisa ka'ida ba har na naira biliyan hudu. Amma kuma daga baya ta dakatar da binciken.

Idan za mu tuna, wata babbar kotun tarayya da ke zama a Kano a watan da ta gabata, ta yi watsi da rahoton hukumar inda ta zargi sarkin da damfarar naira biliyan 3.4 daga cikin kudin masarautar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel