An fi kama turawa da laifin ta'addanci fiye da sauran mutane na duniya - Bincike

An fi kama turawa da laifin ta'addanci fiye da sauran mutane na duniya - Bincike

- Rahotanni sun bayyana cewa yawan Turawa da ake kamawa da laifin ta'addanci yafi na sauran mutanen duniya yawa

- A shekarar 2019 an kama Turawa 117, mutanen yankin Asiya 111, sai kuma bakar fata 21

Yawan Turawan da aka kama a kasar Birtaniya da laifin ta'addanci ya kara linka yawan mutanen yankin Asiya a karo na biyu.

Bayanai sun nuna cewa an kama Turawa 117 a shekarar 2019 da laifin ta'addanci, inda kuma aka kama mutanen yankin Asiya 111, sai kuma bakar fata 21.

Wannan canji ya zo ne bayan jami'an 'yan sanda sun kara karfafa bincike akan masu tsattsauran ra'ayi.

An haramta kungiyar Na-zi a shekarar 2016, amma kuma sai suka tarwatse suka kafa wasu kungiyoyi masu sunaye daban-daban, inda daga baya aka dinga kama 'yan wannan kungiyar.

Shugaban hukumar 'yan sanda masu yaki da ta'addanci na kasar Birtaniya ya bayyana akidar tsattsauran ra'ayi a matsayin babbar barazana ta ta'addanci a kasar ta Birtaniya.

KU KARANTA: Bidiyo: Baturiya ta kama aikin tukin motar haya don ta samu na kashewa a kasar Ghana

Daga watan Maris na shekarar 2017 zuwa yanzu an dakile hare-haren ta'addanci guda 25. Sannan an kama mutane 280 da laifin ta'addanci a shekarar 2019.

Kasa da kashi daya cikin uku na wadanda aka kama an yanke musu hukunci, yayin da kashi 39 kuma aka sake su domin cigaba da bincike a kansu, kashi 23 kuma an sake su ba tare da wani bincike ko hukunci a kansu ba.

A watan Disambar shekarar 2019, akwai mutane 231 a gidan yari da ake zargi da laifin ta'addanci a kasar ta Birtaniya.

Yawancin su ana yanke musu hukuncin shekaru hudu ne a gidan yari, inda daya kuma daga cikinsu aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel