Bidiyo: A daren mu na farko na gano cewa Aljani na aura, bayan ya bace sama da kasa mun rasa shi - Amarya ta koka

Bidiyo: A daren mu na farko na gano cewa Aljani na aura, bayan ya bace sama da kasa mun rasa shi - Amarya ta koka

Wata mata mai suna Gifty Nuname, mai shekaru 32, ta bayyana yadda mijinta ya bata sama da kasa aka neme shi aka rasa bayan auren su

Matar ta bayyana hakane a wata hira da tayi da Y'asem Nie a Adom FM, inda ta bayyana cewa bayan shekara biyu da bacewar mijinta ba su kara jin duriyarshi ba kawai sai ganin gawarshi suka yi.

Bayan sun shafe shekaru masu yawa suna soyayya da saurayin nata mai suna Stephen, Gifty Nuname sun yanke shawarar aure, suka yi ta tara kudi na tsawon shekaru biyu domin wannan biki na su.

Bidiyo: A daren mu na farko na gano cewa Aljani na aura, bayan ya bace sama da kasa mun rasa shi - Amarya ta koka

Bidiyo: A daren mu na farko na gano cewa Aljani na aura, bayan ya bace sama da kasa mun rasa shi - Amarya ta koka
Source: Facebook

An ruwaito cewa duka su biyun sun samu matsalar rashin kudi a lokacin da suke shirin auren nasu.

Kwana daya saura bikin, masoyan suka tafi wani daki a cikin coci suka kwana, inda suka bar wa surukar amaryar dakinsu domin ta kwana a ciki.

Nuname ta bayyana a cikin hirar da suke yi cewa, surukartan na sanya ido akan dan tan sai ta fara kuka, inda take cewa bata son halin da yake a yanzu.

Haka ana saura kwana daya daurin auren nasu sai ga wasu kannan mijin nata mata guda biyu sun bayyana. Sun yi ta zagin ta suna yi mata habaici ba tare da wani dalili ba.

KU KARANTA: Tirkashi: Saurayi ya yiwa budurwarshi tsirara a cikin jama'a saboda taki yadda ta aure shi

Bayan daurin aure, sai suka koma dakin da suke zama na cikin cocin, sai Stephen ya ci wani abinci da 'yan uwanshi suka bar mishi saboda yana jin yunwa sosai.

Nuname ta ce ta tashi a firgice daga bacci bayan Stephen yayi wata kara da bata taba jin irinta ba.

Hakan yasa ta fara addu'a, amma sai ta ga cewa addu'ar tan bata aiki, sai ta fita da gudu ta kira fasto domin ya taimaka mata.

"Faston ya dan shawo kanshi yace yaje ya saka kaya ya rufe jikin shi a wani daki, amma yana cikin dakin sai muka ji wata kara kuma, muna zuwa dakin sai muka ga babu kowa a ciki sai takalmin shi ya bace," in ji ta.

Cikin kuka Nuname ta ce duka kofofin wajen a kulle suke babu ta yadda za ayi mutum ya bar wannan wuri ba tare da an ganshi ko kuma anji motsin shi ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel