Jaruma Samira Ahmad ta gina famfon tuka-tuka a makarantar sakandire da ta gama a Jogana
- Fitacciyar jarumar Kannywood Samira Ahmad ta gina sabon famfon tuka-tuka a tsohuwar makarantar da ta kammala a garin Jogana
- Samira Ahmad ta kammala makarantar a shekarar 2005, inda a lokacin tana daya daga cikin dalibai masu hazaka na makarantar
- Jarumar ta bukaci daliban makarantar da duk abinda suka zama a rayuwa kada su manta da makarantar su
Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Samira Ahmad ta gina sabuwar rijiyar burtsatse (Tuka-Tuka) a tsohuwar makarantar sakandiren da ta kammala ta Government Girls Secondary School Jogana dake cikin jihar Kano.
Samira Ahmad wacce ta kammala makarantar ta kwana a shekarar 2005, tana daya daga cikin 'yan kungiyar Hausa na makarantar, kuma tana daya daga cikin masu ilimi sosai a makarantar.
Da take gabatar da rijiyar burtsatsen a wajen dakunan daliban dake makarantar, jaruma Samira Ahmad ta bukaci daliban da a koda yaushe su dinga tinawa da makarantar da suka yi koda sun zama wasu a nan gaba.
KU KARANTA: Na cika da mamaki dana ga sunana cikin fitattun mutane a Kano - Nazifi Asnanic
Ta kara da cewa daya daga cikin manyan matsalolin da daliban makarantar sakandare ta kwana suke fuskanta ita ce rashin ruwa, musamman a karshen mako, sannan kuma ta yi kira ga sauran daliban dasu hada karfi da karfe wajen kawo cigaba a makarantun jihar ta Kano.
Makarantar matan ta garin Jogana dake jihar Kano tana daya daga cikin manyan makarantu a jihar Kano, kuma tana daya daga cikin makarantun da gwamnatin jihar Kano za ta gyara.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng