Jami’an tsaro sun kama Ronaldinho da Kaninsa da fasfon bogi a Paraguay

Jami’an tsaro sun kama Ronaldinho da Kaninsa da fasfon bogi a Paraguay

Rahotanni sun zo mana cewa an kama fitaccen tsohon ‘Dan wasan Duniya Gaucho Ronaldinho da laifin amfani da takardu na bogi a kasar waje.

Kamar yadda labari ya zo mana dazu, Gaucho Ronaldinho, ya na tsare ne a kasar Paraguay, bayan an same shi da takardun shiga kasa na bogi.

Ana zargin cewa akwai alamun tambaya game da takardun da tsohon ‘Dan wasan na kasar Brazil ya yi amfani da su wajen zuwa kasar Paraguay.

Gaucho Ronaldinho ya ziyarci kasar Amurkan ne a sakamakon wata gayyata da Nelson Belotti ya yi masa. Belotti sanannen mutum ne a Yankin.

Ronaldinho ya sa kafa ne a kasar Paraguauy a Ranar Laraba, 4 ga Watan Maris. Jim kadan da zuwansa Garin, jami’an tsaro su ka yi ram da shi.

Rahotannin kasashen ketaren sun nuna cewa an kama Ronaldinho ne a dakin da ya sauka. Tauraron ya zo da niyyar halartar wani taro ne kasar.

KU KARANTA: Ronaldinho ya yi ritaya da buga kwallo a Duniya

Jami’an tsaro sun kama Ronaldinho da Kaninsa da fasfon bogi a Paraguay
Jami’an tsaron Paraguay su na zargin Ronaldinho da amfani da fasfon karya
Asali: Facebook

Jaridar The Telegraph ta bayyana cewa jami’an tsaron sun yi wa tsohon ‘Dan kwallon tambayoyi game da takardar fasfon da ya ke amfani da shi.

Kafin hakan ya faru, tsohon ‘Dan kwallon na Barcelona da Tawagarsa sun yi niyyar ganawa da ‘Yan jarida da kuma Masoyansu da ke kasar Paraguay

Jaridar La Nacion ta ce an damke Tauraron mai shekaru 39 a Duniya ne a wani otel da ake kira Resort Yacht & Golf Club Paraguayo da ke cikin kasar.

Ronaldinho ya na tare da wani ‘Danuwansa Roberto wanda ake zarginsu tare da yin karyar cewa su ‘yan kasa ne a cikin fasfon da su ke dauke da shi.

Majiyar ta ce ana yi wa ‘Yan kasar Brazil din tambayoyi ne kawai, daga nan ne za a san cewa za a tsare su ko kuma ba za a dauki wani mataki ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel