ICPC ta gano Naira Biliyan 594 da wasu Ma’aikatan Gwamnati su ka sace

ICPC ta gano Naira Biliyan 594 da wasu Ma’aikatan Gwamnati su ka sace

Hukumar ICPC mai yaki da Barayi da masu satar dukiyar gwamnati ta ce ta gano wasu makudan kudi da ta ke zargin an sace daga asusun gwamnatin Najeriya.

A cewar jaridar kasar nan ta The Nation, ICPC ta bayyana cewa ta na zargin an sace wadannan dukiya ne daga shekarar 2016 zuwa shekarar bara watau 2019.

Hukumar ta ce ta karbo kudin ne daga hannun tsofaffin ma’aikatan da su ka yi wa gwamnatin Najeriya aiki a karkashi hukumomi da ma’aikatun da ake da su.

Rahotannin sun bayyana cewa wadannan tsofaffin ma’aikata sun cigaba da karbar albashi bayan sun yi ritaya daga aiki. Wannan dai ya sabawa dokokin Najeriya.

Haka zalika akwai wadanda su ke bakin aiki a yanzu, amma an same su da laifin karbar albashi biyu. Johnson Oludare da ke aiki da hukumar ya fallasa wannan.

KU KARANTA: Hukumar AMCON za ta yaki wadanda ba su biyan bashin banki

ICPC ta gano Naira Biliyan 594 da wasu Ma’aikatan Gwamnati su ka sace

Hukumar ICPC ta na yaki da masu satar dukiyar kasa a Najeriya
Source: UGC

Oludare wanda Mataimakin Darekta ne da ke kula da binciken kudi a hukumar ICPC ya yi jawabi ne a wajen taron da wata cibiyar Afrika ta shirya a Garin Minna.

Wannan cibiya mai alhakin koyar da harkar yada labarai ta shirya wani taro ne da ya tattauna game da tsarin da gwamnati ta kwadaitar na tona asirin barayi.

“N594,089,136,242 mu ka karbe daga tsofaffin ma’aikata 800 da su ka ciba da karbar albashi, da kuma ma’aikata 400 da su ke karbar albashi biyu a bakin aiki.”

“Akwai kuma ma’aikata 1200 da su ka hada kai da kananan bankuna su ka saci kudi daga asusun ma’aikatu da hukumomin gwamnati tsakanin 2016 da 2018.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel