An kama dan sanda mai mukamin sufeta da ya bindige wani farar hula har lahira

An kama dan sanda mai mukamin sufeta da ya bindige wani farar hula har lahira

Rundunar ‘yan sandan jihar Edo a ranar Laraba, ta ce ta damke sifetan ‘yan sanda wanda ake zarginsa da harbin wani farar hula mai suna Richard Odia a Benin.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Chidi Nwabuzor, ya bayyana haka a takardar da ya ba Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya a Benin.

Nwazubor ya ce kwamishin ‘yan sandan jihar, Lawan Jimeta ya bada umarnin ladabtarwa ta gaggawa ga sifetan ‘yan sandan.

Ya yi bayanin cewa, sifetan yana aiki ne a karkashin rundunar ‘yan sandan da ke jihar Delta inda yake karkashin runduna ta musamman ta 301 da ke kamfanin Asaba.

Mai magana da yawun rundunar ya ce, dan sandan na aiki ne daga Asaba zuwa Benin lokacin da yayi harbin kuma ya kashe mutum. Ya ce lamarin ya faru ne a ranar 11 ga wata Fabrairu wajen karfe 7 na yammaci.

An kama dan sanda mai mukamin sufeta da ya bindige wani farar hula har lahira
An kama dan sanda mai mukamin sufeta da ya bindige wani farar hula har lahira
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan Boko Haram sun kai hari Dapchi suna kona gidaje

Kamar yadda Nwabuzor ya sanar, dan sandan ya yi harbin ne tare da raunata mamacin da bindiga mai kirar AK-47 a kan babbar hanyar Benin zuwa Auchi bayan sun samu dan rashin jituwa.

“An hanzarta kai mutumin asibitin koyarwa na jami’ar Benin amma sai ya mutu a ranar 12 ga watan Fabrairu. Kwamsihinan ‘yan sandan jihar, Lawan Jimeta ya yi wa iyalan mamacin ta’aziyya a kan mutuwarsa. Kuma ya kara da tabbatar musu da cewa za a kwatar musu ‘yancinsu.” Ya ce.

Ya kara da mika bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali ga jama’ar da ke yankin kuma su kara da mutunta rayukan jama’a.

Yana kuma gayyatar duk mai shaida a kan aukuwar lamarin da ya garzaya don bayar da gamsassun shaidun da za su taimaka wajen bincike har zuwa yanke hukunci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel