Na cika da mamaki dana ga sunana cikin fitattun mutane a Kano - Nazifi Asnanic

Na cika da mamaki dana ga sunana cikin fitattun mutane a Kano - Nazifi Asnanic

- Fitaccen mawakin nan mazaunin jihar Kano, Nazifi Asnanic ya nuna mamakin shi ta yadda sunan shi ya shiga jerin mutane sanannu 10 na jihar kano

- Jerin mutanen sun hada da Aliko Dangote, Sanusi Lamido Sanusi, Aminu Dantata, Aminu Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Amina Namadi Sambo da sauransu

- Ya bayyana cewa wannan daukaka ce babba gareshi ta yadda ya shiga cikin sunayen su Dangote a jerin

Sannanen mawaki Nazifi Abdulsalam Yusuf wanda aka fi sani da Nazifi Asnanic ya nuna mamakinsa kan yadda aka saka shi a cikin jerin fiitattun mutane 10 na jihar Kano baki daya.

A ranar Lahadin 23 ga watan Fabrairun 2020, wata mujalla mai suna Guide Nigeria ta walafa jerin da ta kira fitattun mutane 10 na jihar Kano inda ta lissafa har da nazifi Asnanic da ya bayyana a na shida.

Na cika da mamaki dana ga sunana cikin fitattun mutane a Kano - Nazifi Asnanic
Na cika da mamaki dana ga sunana cikin fitattun mutane a Kano - Nazifi Asnanic
Asali: Twitter

Jerin mutanen sun hada da Aliko Dangote, Sanusi Lamido Sanusi, Aminu Dantata, Aminu Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, Amina Namadi Sambo da sauransu.

A hirar mawakin da mujallar fim, ya nuna farin cikin shi kan wannan lamarin.

“Gaskiya ni da na fara jin labarin a farko, na dauka shirme ne kawai. Sai da na ga abin ya fara zarya a kafafen sada zumuntar zamani na yadda. Sai da hankalin na ya dawo ne nayi wuf na nemi daga inda labarin ya fito. Bayan na gani ne nake mamakin yadda sunana ya shiga cikin na su Dangote.”

KU KARANTA: Tirkashi: Saurayi ya yiwa budurwarshi tsirara a cikin jama'a saboda taki yadda ta aure shi

Ya kara da cewa, “A cike da mamaki kuwa da farin ciki nake nuna jin dadi na. Wannan babban ci gaba ne a rayuwata.”

Sanannen mawakin ya yi fatan alheri da jinjina ga jihar Kano a kan irin ci gaban da ake samu wajen daga darajar addinin Musulunci.

Ya kara da yin godiya ga masoyan shi a kan karfin guiwar da suke bashi tare da goya mishi baya, “saboda idan babu su toh babu ni. Na gode kwarai.” Cewar Asnanic.

Daga karshe kuwa, ya yi wa masoyan nashi albishir da cewa kwannan nan zai sako musu ci gaban shahararriyar wakar nan tasa mai taken ‘Labari Na’ wacce yake kan aikinta yanzu haka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng