Sanatan APC ya yi Alla wadai da mulkin dimokradiyya, ya yabi mulkin soji

Sanatan APC ya yi Alla wadai da mulkin dimokradiyya, ya yabi mulkin soji

An samu dimuwa da kuma al’ajabi a zauren majalisar dattijai a ranar Laraba yayin da sanatan APC mai wakiltar jihar Kogi ta yamma, Smart Adeyemi ya sanar da cewa ya fi son mulkin soja a kan irin mulkin damokaradiyyar da ake yi a Najeriya.

Wannan lamarin kuwa ya kawo guna-guni tare da cece-kuce daga ‘yan uwansa ‘yan majalisar inda suka soki wannan ra’ayin tare da kwatanta shi da mai sukar damokaradiyya.

Adeyemi ya sanar da hakan ne yayin da yake bada gudumawa a kan kirkiro sabuwar doka a kan laifukan zabe wanda Sanata Abubakar Kyari ya mika gaban majalisar.

Kyari ya ce hukumar zaben mai zaman kanta na azarbabin daukar mataki kan masu laifukan zabe, amma don hakan ne ya kamata a samar da hukuma mai kula da hakan.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya gargadi Adeyemi a kan hakan tare da cewa hakan ba wakilci nagari bane ga yankinsa da kuma majalisar baki daya.

Sanatan APC ya yi Alla wadai mulkin dimokradiyya, ya yabi mulkin soji
Sanatan APC ya yi Alla wadai mulkin dimokradiyya, ya yabi mulkin soji
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan darikar 'Faidha' da ake zargi da yin wakar batanci ga Annabi sun tsallake rijiya da baya

Sauran sanatocin da suka hada da James Manaja da George Seikibo, sun musanta ikirarin Adeyemi tare da jaddada cewa mulkin damokaradiyya ya fi na gwamnatin soji.

A fusace Adeyemi ya jajanta yadda ake mulkin damokaradiyya a Najeriya ballantana yadda zabe ke tafiya babu tsari.

Ya ce, “Babu wani tunani ko bata lokaci, zan iya cewa babu damokaradiyya a duk kasar da babu zabe na gaskiya mai inganci. Za a iya samun badakallar kudade da shugabancin kama-karya. Duk muna fuskantar hakan ne kuwa saboda matsalar zabe a kasar nan. A ta hakan ne mutanen da basu dace ba suke samun damar hayewa mulki.”

A wannan lokacin ne shugaban majalisar dattijan ya katse shi tare da tunatar masa da shi cewa a halin yanzu Najeriya na mulkin damokaradiyya ne.

Sanata George Seikibo ya nuna tsananin damuwarsa tare da bayyanawa sanatan jihar Kogin ta yamma din bai dace ba ya bayyana cewa yafi son mulkin soja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng