An yi ruwan gawarwaki bayan an shafe sa'a biyar ana musayar wuta da sojoji da 'yan Boko Haram a Borno

An yi ruwan gawarwaki bayan an shafe sa'a biyar ana musayar wuta da sojoji da 'yan Boko Haram a Borno

Dakarunnrundunar sojin Najeriya sun yi nasarar fatattakar mayakan kungiyar ISWAP a Damboa bayan shafe sa'a biyar ana musayar wuta a yau, Laraba, 4 ga watan Maris, 2020.

A cewar dan jarida mai gudun hijira, Ahmad Salkida, gawarwakin mayakan kungiyar sun mamaye kusan ko ina a filin da suka yi musayar wuta da sojoji.

Salkida ya bayyana cewa mayakan da suka rage sun gudu sun bar motocinsu na yaki guda 18.

Kazalika, wasu daga cikin jami'an tsaro, mambobin kungiyar sakai (civilian JTF) da maharba sun rasa ransu yayin doguwar musayar wutar, kamar yadda Salkida ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta, tuwita (@)_Salkida).

Da safiyar ranar Laraba ne Legit.ng ta wallafa rahoton cewa jama'ar garin Damboa, hedikwatar wata karamar hukuma a jahar Borno, na karkashin harin yan ta’addan Boko Haram.

DUBA WANNAN: Mataimakin shugaban APC na yankin arewa ya bayyana dalilin jin dadin dakatar da Oshiomhole

Mazauna yankin sun ce yan ta’addan sun zo su da yawa da misalin karfe 6:30 na safiyar ranar Laraba, 4 ga watan Maris sanan suka fara harbi ba kakkautawa, kamar yadda jaridar TheCable ta ruwaito.

Daya daga cikin mazauna yankin ya ce sama da sa’a daya, sojoji daga bataliya ta 25 a Damboa na ta musayar wuta da yan ta’addan.

Sun zo su da yawa a motocin hilux kimanin su 20, hakan yasa muka fara gudu zuwa cikin daji domin tsira da ranmu,” a cewar daya daga cikin mazauna yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel