Malami: Har yanzu ba a dawowa Gwamnatin tarayya da kudin satar Abacha ba

Malami: Har yanzu ba a dawowa Gwamnatin tarayya da kudin satar Abacha ba

Ministan shari’an Najeriya, Abubakar Malami (SAN), ya ce ragowar kudin satar Marigayi Janar Sani Abacha ba su kai ga shigowa hannun gwamnatin tarayya ba.

Abubakar Malami ya bayyana wannan ne a Ranar Talata, 3 ga Watan Maris a Abuja. Ministan kasar ya yi jawabi ne ta bakin wani Hadiminsa, Dr. Umar Gwandu.

Umar Gwandu ya karyata zargin da jam’iyyar PDP ta ke yi na cewa jami’an gwamnati sun sake wawurar wannan kudin sata da aka maidowa gwamnatin Najeriya.

Da Ministan shari’an kuma babban Lauyan gwamnatin kasar ya ke bayani ta bakin Mai taimaka masa wajen hula da jama’a, Umar Gwandu, ya ce kudin ba su shigo ba.

Malami SAN ya ke cewa kudin da ake sa rai daga kasar Amurka da kuma New Jessy ba su kai ga shigowa hannun gwamnatin tarayyar Najeriya ba har zuwa jiya Talata.

“Saboda haka maganar karkatar da kudin ko kuma batar da su, kanzon kurege ne kurum domin ba a dawo da kudin ba ma tukuna ga asusun Najeriya.” Inji Ministan.

KU KARANTA: Abacha: Najeriya ta na kokarin biyan Gwamnan Kebbi $100m a boye

Malami: Har yanzu ba a dawowa Gwamnatin tarayya da kudin satar Abacha ba

Abubakar Malami ya ce kudin satar Abacha ba su zo hannun Gwamnatin tarayya ba
Source: Depositphotos

Haka zalika Ministan shari’an ya yi karin haske da cewa duk kudin da gwamnatin Buhari ta karbe daga hannun Barayi, sun yi amfani ne wajen taimakon al’umma.

Ministan ya bada tabbacin cewa ayyukan da za su amfani Talaka ake yi da kudin satar da shugaba Muhammadu Buhari ya samu a hannun Barayin Najeriya.

Kafin yanzu an dawowa Najeriya wasu makudan kudi da ake zargin cewa tsohon shugaban kasar, Janar Sani Abacha ne ya sace, ya kuma boye su a kasashen ketare.

Kwanakin baya gwamnatin tarayyar ta sa hannu a wata yarjejeniya da kasar Amurka da New Jersey domin dawowa Najeriya da wasu kudinta fam dala miliyan 300.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit Newspaper

Online view pixel