Aikinka na kyau: Hukumar FBI ta Amurka ta karrama Magu da lambar yabo

Aikinka na kyau: Hukumar FBI ta Amurka ta karrama Magu da lambar yabo

Mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, Ibrahim Magu ya samu kyautar lambar yabo daga hukumar binciken kwakaf ta kasar Amurka, FBI.

Daily Nigerian ta ruwaito FBI ta karrama Magu da lambar karramawar ne a ranar Talata, 3 ga watan Maris, a ofishinsa dake sakatariyar hukumar EFCC dake babban birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Riga kafi ya fi magani: An fara tantance masu ziyarar fadar shugaban kasa don gudun Coronavirus

Aikinka na kyau: Hukumar FBI ta Amurka ta karrama Magu da lambar yabo

Aikinka na kyau: Hukumar FBI ta Amurka ta karrama Magu da lambar yabo
Source: Facebook

Jami’in shari’a na hukumar FBI a Najeriya, Ahamdi Uche ne ya mika ma Magu wannan lambar yabo a madadin hukumar FBIinda ya ce Magu ya cancanci wannan karramawa ne duba da rawar da ya taka a wani aikin yaki da rashawa na musamman da FBI ta shirya mai taken “Operation Rewired”.

Shi dai wannan aiki na “Operation Rewired” FBI ta kirkireshi ne domin yaki da satar kudi da rashawa ta hanyar yanar gizo, haka zalika Ahamdi ya jinjina ma Magu bisa kwarewarsa wajen tafiyar da shugabanci tare da kokarin hukumar EFCC a yaki da rashawa.

Aikinka na kyau: Hukumar FBI ta Amurka ta karrama Magu da lambar yabo

Aikinka na kyau: Hukumar FBI ta Amurka ta karrama Magu da lambar yabo
Source: Facebook

A wani labari kuma, fadar shugaban kasar Najeriya ta fara gudanar da tantance ma’aikata da kuma bakin dake ziyartar fadar dake babban birnin tarayya Abuja biyo bayan samun bullar annobar cutar Coronavirus mai suna COVID-19 a Najeriya a ranar juma’ar da ta gabata.

An tura jami’an kiwon lafiya a kofar karshe ta shiga ofisoshin dake cikin fadar shugaban kasa don su tabbatar ma’aikatan fadar gwamnatin tare da baki masu kai ziyara sun wanke hannayensu da ruwan wanke hannu na musamman domin kashe kwayoyin cututtuka dake hannuwan.

Haka zalika jami’an kiwon lafiyan suna amfani da na’urar gwada zafin jikin mutum domin gwajin yanayin zafin ma’aikatan Villa da kuma baki, daga cikin wadanda aka yi ma wannan gwaji a ranar Talata akwai ministan kwadago, Chris Ngige wanda ya isa fadar da misalin larfe 4:50 na rana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel