Gagararrun masu garkuwa da mutane 6 sun fada komar jami’an Yansanda

Gagararrun masu garkuwa da mutane 6 sun fada komar jami’an Yansanda

Kwana dubu na barawo, kwana daya rak na mai kaya kamar yadda kwamishinan Yansandan jahar Delta, Hafiz Inuwa ya sanar da kama wasu miyagun mutane masu sata tare da garkuwa da jama’an da basu ji ba, basu gani ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito kwamishina Inuwa ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Warri inda yace Yansanda sun kama barayin ne a tsakanin ranakun Lahadi da Litinin a Oghara, karamar hukumar Ethiope ta yamma.

KU KARANTA: Ilimi gishirin zaman duniya: Mataimakin gwamnan Kogi ya koma makaranta

A cewar kwamishinan, mutane hudu daga cikinsu sun amsa laifin satar wata mata mai suna Victoria Okereka daga asibitinta a ranar 22 ga watan Feburairu, wanda suka saketa bayan ta kwashe kwana guda a hannunsu.

Amma kwamishinan yace suna cigaba da gudanar da bincike don sanin iya barnar da sauran miyagun biyu suka tafka a jahar. Inuwa ya ce sun kwato wukake 2, bindga, da kuma wayoyin salula da dama.

“Daga ranar Lahadi zuwa Litinin, mun kama wasu miyagu, kuma dukkaninsu suna cikin gungun barayin mutane, an tabbatar da guda hudu daga cikinsu. An gano su, kuma sun amsa laifukansu, amma muna cigaba da binciken sauran mutane biyu.” Inji Inuwa.

A wani labarin kuma, tsohon gwamnan jahar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bara game da zargin da ake yi masa da hannu cikin badakalar kudin makamai a zamanin da yake minista, sa’annan ya wanke manyan hadimansa guda biyu, Injiniya Abba Kabir Yusuf da Abdullahi Umar Ganduje.

A makon nan ne wasu rahotanni daga jaridu daban daban suka bayyana cewa hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta kaddamar da bincike a kan badakalar kwangilar sayo makamai da aka yi a ma’aikatar tsaro a shekarar 2008.

Sai dai Kwankwaso ya kasance ministan tsaro ne daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2006, kamar yadda tsohon gwamnan ya tabbatar da kansa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel