Masarautar Kebbi ta bawa Lai Mohammed sarautar gargajiya

Masarautar Kebbi ta bawa Lai Mohammed sarautar gargajiya

A ranar Talata ne masarautar Kebbi ta karrama ministan yada labarai da al'adu, Lai Mohammed, da sarautar gargajiya mai lakabin "Kakakin Kebbi" (jakadan kebbi na al'adu a Najeriya da ketare.)

Sarkin Argungu, Sama'ila Mera, ya sanar da hakan a Abuja bayan ya mika takobin nadin sarauta ga minisatan tare da saka masa kayan sarauta.

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) ya rawaito cewa takaitaccen bikin nadin sarautar yana daga cikin shirin taron manema labarai na shekarar 2020 a kan bikin kamun kifi na Argungu karo na 60.

"Mun yanke shawarar yi maka wannan karramaw ane domin nuna godiya ga kokarinka na raya mabanbantan al'adun da ke Najeriya tare da samar da guraben aiyuka da kuma wayar da kan matasanmu a kan gadonmu da mutunta bukukuwanmu na al'ada.

Masarautar Kebbi ta bawa Lai Mohammed sarautar gargajiya

Lai Mohammed
Source: Depositphotos

"Mun jinjina wa kishinka na kasa da kuma yadda ka ke kare kima da martabar kabilu da al'adun Najeriya da kuma sauken nauyin da ke tattare da ofishinka.

DUBA WANNAN: Yadda tsofin gwamnonin jihohin arewa uku suka kirkiri Boko Haram - Musa Dikwa

"Bikin kamun kifi na Argungu da aka saba yi duk shekara ya shiga ciki jerin bukukuwan duniya na al'ada da hukumar kasa da kasa; 'UNESCO' ta san da zamansu," a cewar sarkin.

Mera ya ce masarautarsa ta amince da karrama Mohammed ne yayin wani zama na musamman tsakanin majalisar zartar wa ta masarautar da mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Samaila Yombe, wanda aka yi ranar Laraba ta makon jiya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel