Janar Babagana Monguno ya halarci taron kwamitin harkar makamai

Janar Babagana Monguno ya halarci taron kwamitin harkar makamai

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa an shirya wani taro na musamman na kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin kula da sha’anin makamai.

Daga cikin wadanda su ka halarci wannan zama na jiya akwai Mai ba shugaban kasa shawara a kan harkar tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno mai ritaya.

A baya an yi ta rade-radin cewa an samu sabani tsakanin Janar Babagana Monguno da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa watau Malam Abba Kyari.

Sauran ‘yan wannan kwamiti na shugaban kasa sun hada da Ministan shari’a kuma babban Lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da wasu Ministoci.

Ministan harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola da kuma Ministan harkokin kasashen waje, Geoffrey Onyeama, su na cikin ‘yan wannan kwamitin tsaro.

KU KARANTA: Ana kashe Musulmai a Garin Delhin Kasar Indiya

Janar Babagana Monguno ya halarci taron kwamitin harkar makamai

Yemi Osinbajo ya jagoranci kwamitin shiga da ficen makamai
Source: Twitter

Sauran wadanda aka yi wannan taro da su sun hada da: Shugaban hukumar DSS masu fararen kaya, Yusuf Magaji Bichi wanda aka nada a Satumban 2018.

Jaridar ta ce Shugaban hukumar NIA masu leken asiri, Ambasada Ahmed Rufai Abubakar ya halarci zaman tare da CDI AVM Mohammed Saliu Usman.

Shugaban hukumar kula da fasa-kauri, Hameed Ali ya na cikin kwamitin da shugaba Buhari ya nada domin ya duba safarar kanana da matsakaitan makamai.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo shi ne ke shugabantar wannan kwamiti. Najeriya ta na cikin kasashen da makamai su ka fada hannun gama-gari.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel