EFCC ta cafke wata mata da ta damfari Hadiza Inna Sanusi N36m a Kano
A ranar Talata ne hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta gurfanar da wata mata mai suna Asiya Bala Aliyu, a gaban wata babbar kotu da ke jihar Kano, bisa tuhuma guda biyu da suka hada da damfara da karkatar da kudade.
A cikin jawabin da shugaban sashen yada labarai da sanarwa a hukumar EFCC, Tony Orilade, ya fitar, ya bayyana cewa Asiya ta karbi kudi, miliyan N36, daga hannun Hadiza Inna Sanusi da sunan saka hannun jari a wani tsarin kasuwanci mai suna 'Galaxy Investment Package'.
Sai dai, Asiya ta karkatar da kudin da ta karba tare da yin amfani da su wajen kashe matsalolin kanta.
Daya daga cikin tuhumar na cewa: "ke, Asiya Bala Aliyu, a wani lokaci da ya wuce, tsakanin watan Mayu da Agusta na shekarar 2018, kin karbi kudi miliyan talatin da biyar (N35,000,000) daga hannun Hadiza Inna Sanusi, da sunan saka jari a wata harkar kasuwanci, amma kika nuna rashin gaskiya tare da lalata kudin da kika karba. Yin hakan ya saba da sashe na 308 kuma an tanadi hukucinsa a karkashin sashe na 309 na kundin dokoki da hukuncin laifuka."
Sai dai, wacce ake gurfanar din ta ki amincewa da tuhumar da ke yi mata a gaban kotun.
Lauyan hukumar EFCC, Musa Isah, ya roki kotun ta saka ranar fara shari'a da Asiya domin tabbatar wa da alkali cewa tana da laifi.
Khalid Kashim Njidda, lauyan da ke kare wacce ake kara, ya mika bukatar neman kotu ta bayar da belin wacce ya ke kare wa.
DUBA WANNAN: Imo: Kotun koli ta yi watsi da bukatar sake duba hukuncin kwace kujerar gwamnan PDP
Sai dai, lauyan EFCC ya soki bukatar neman bayar da belin Asiya. Kazalika, ya soki bukatar neman a tsare ta a ofishin EFCC har zuwa lokacin zaman kotun na gaba, kamar yadda lauya Njidda, da ke kare Asiya, ya nema.
Alkalin kotun, Jastis R. A Sadiq, ya amince da bukatar lauyan hukumar EFCC tare da saka ranar 12, ga watan Maris, 2020 domin sauraron bukatar neman baya da belin Asiya tare da fara shari'ar tuhumar da ake yi mata.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng