Imo: Kotun koli ta yi watsi da bukatar sake duba hukuncin kwace kujerar gwamnan PDP

Imo: Kotun koli ta yi watsi da bukatar sake duba hukuncin kwace kujerar gwamnan PDP

Kotun koli ta y watsi da bukatar sake duba hukuncin da ta yanke na kwace kujerar gwaman jihar Imo daga hannun Emeka Ihedioha na jam'iyyar PDP tare da bayar da umarnin mika ta ga Hope Uzodinma na jami'iyyar APC.

Da take yanke hukunci ranar Talata a kan bukatar sake duba hukuncin, kotun; mai alkalai bakwai a karkashin jagorancin alkalin alkalai na kasa (CJN), Tanko Muhammad, ta bayyana cewa ba ta da ikon sake zama domin sauraron daukaka karar neman ta sake duba hukuncin da ta yanke da kanta.

Da yake karanta hukuncin kotun, Jastis Olukayode Ariwoola, ya bayyana cewa bukatar sake duba hukucin bata da matsuguni a tsarin shari'a, a saboda haka sun yi watsi da ita.

Imo: Kotun koli ta yi watsi da bukatar sake duba hukuncin kwace kujerar gwamnan PDP
Hope Uzodinma yayin yakin neman zabe a 2019
Asali: Facebook

Alkalin ya bayyana cewa kotun ba zata ci tarar masu kara ba tare da bayyana cewa babu wata sarkakiya ko baki biyu a hukuncin da kotun kolin ta yanke da farko a ranar 14 ga wata Janairu.

DUBA WANNAN: Yadda tsofin gwamnonin jihohin arewa uku suka kirkiri Boko Haram - Musa Dikwa

A cikin takardar daukaka kara da jam'iyyar PDP da tsohon gwamna Ihedioha suka shigar a ranar 5 ga watan Fabrairu, sun bukaci kotun kolin ta sake duba hukuncin da ta yanke na kwace kujerar gwamna daga hannunsu a zaben ranar 9 watan Maris, 2019, da hukumar INEC ta bayyana sun samu nasarar lashe wa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng