Harin Igabi: Akalla gawawwakin mutane 50 aka tsinta a jihar Kaduna

Harin Igabi: Akalla gawawwakin mutane 50 aka tsinta a jihar Kaduna

An tsinci akalla gawawwaki 50 a harin da aka kai a kauyukan dake karamar hukumar Igabi a Jihar Kaduna.

A wani tattaunawa da VOA tayi da wani mai gadin kauye, yace harin ya faru ne a safiyar Lahadi.

Yace yan bindigan sun kona gidaje,ababen hawa da wasu gawawwaki.

Bisa ga bayanin mai gadin, yan bindigan sun fara kai hari kauyen Marina ne dake karamar hukumar inda suka kashe mutane da yawa kafin su shiga kauyen Kerawa.

“An kawo mana hari ne a safiyar Lahadi. Akwai wani kauye da ake kira Marina, yan bindigan sun fara tatike kauyen ne, babu wani mahaluki yanzu a kauyen. Sun kashe mutane da yawa har da yara, a yanzu akwai gawawwaki 50,” A cewar shi.

“Sun kai awanni uku suna aika-aika, ba wani dan sandan da yazo. Sun kona gidaje, kayan masarufi, ababen hawa kuma yi garkuwa da mutane."

"Mun san wurin da suke boye kuma mun dade muna kai kuka akansu. Muna kira ga gwamnati data taimaka mana wurin kawar da wannan matsalar.”

KU KARANTA Za’a hukunta mahaifiyar da ta yiwa danta jina-jina a Legas

Kansila mai wakiltar Kerawa, Daiyabu Kerawa ya jajanta al’amarin kuma yayi kira da a taimaka musu wurin kawar da matsalar.

“Da misalin karfe shida na safiyar Lahadi ne yan bindiga suka shigo kauyen Marina suka zagaye kauyen, suka bi gida-gida suna kashe yara, almajirai har ma da tsofaffi, suna kona su. Akwai mutumin da s ka kona masa gonar dawa sannan suka kashe shi tare da matarsa da yaransa,”A cewar sa.

“A kauyen Kerawa kawai akwai gawawwaki hamsin da ba’a birne ba. Muna kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da ya kawo agaji ga karamar hukumar Igabi ya kawo mana jami’an tsaron da zasu taimaka mana.sun kai hari har kauyuka 13, basu dauki komai ba amma sun kashe mutane sun kona wurare da dama. ”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng

Online view pixel