Suleiman Yusuf: Mai gadin gidan radiyon da ya zama minista

Suleiman Yusuf: Mai gadin gidan radiyon da ya zama minista

Masu hikimar zance sun ce rabon kwado baya taba zama a sama, sai ya sauko kasa. Kuma ba kasafai ake samun labarin cewa mai gadi ya rike mukamin minista a gwamnati ba.

Sai gashi wani mutum mai suna Suleiman Yusuf Koore wanda ya kasance mai gadi a yankin Somaliya, ya zama minista.

An tattaro cewa Koore ya fara aikin gadi a shekarar 1984 a gidan rediyon gwamnatin Hargeisa, wanda ke a cikin ma’aikatar yada labarai ta kasar.

Suleiman Yusuf: Mai gadin gidan radiyon da ya zama minista
Suleiman Yusuf: Mai gadin gidan radiyon da ya zama minista
Asali: UGC

Sai gashi a yanzu shi ne ministan yada labarai na kasar Somaliya, wanda hakan na nufin shine babba a ma’aikatar yada labaran kasar.

Mista Koore ya ce “A lokacin da nake gadi ba a bari na shiga ofishin da nake zama a yanzu a matsayin minista saboda ni mai gadi ne a wancan lokacin”.

A lokacin da yake gadi yana daukar albashin da bai wuci dala 12 ba, amma a yanzu da yake a matsayin minista, albashinsa a wata ya kai dala 2,000 ban da alawus din dala 750 duk wata.

Ministan dai ya dade ana fadi-tashi da shi a harkar siyasar kasar don ya shafe shekara 25 yana harkokin siyasa; haka kuma ya rike mukamai da dama, kafin a ba shi minista yanzu.

Ya kara da cewa “Abin alfahari ne a gare ni na zamo wa minista ama’aikatar da na yi wa aiki a zamanin da nake matashi.”

KU KARANTA KUMA: Ya zama dole mu yi aiki da addu’a don Najeriya ta inganta, In ji Obasanjo

A wani labari na daban, mun ji cewa Dino Melaye, wani tsohon sanata mai wakiltan Kogi ta yamma ya fara fuskantar abubuwa kamar kowa bayan tsohon dan majalisar ya je shafin zumunta don yin korafi a kan abun da ya yi wa lakabi da “nauyin bukatu”.

Melaye ya yi aiki a matsayin sanata a majalisar dattawa ta takwas amma dawowarsa majalisa ta hadu da cikas bayan kaye da ya sha a hannun Smart Adeyemi a zaben da aka sake a yankin Kogi ta yamma.

Tsohon sanatan mai shekara 46, wanda kwanan nan ya mallaki wani katafaran gida, a yanzu yana korafi a kan nauyin bukatunsa da ya ce sun karu, inda dama halinsa me yin barkwanci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel