Ya zama dole mu yi aiki da addu’a don Najeriya ta inganta, In ji Obasanjo

Ya zama dole mu yi aiki da addu’a don Najeriya ta inganta, In ji Obasanjo

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ce sai an hada hannu dukka wajen magance matsalolin tsaro a kasar.

Da ya ke magana a yayin wani ziyarar ban girma da jakadu na musamman, archbishop Justin Welby ya kai masa a Abeokuta, babbar birnin jahar Ogun, Obasanjo ya bayyana cewa ya zama dole dukkanin yan Najeriya su yi aiki da addu’a don dawo da hadin kai a tsakaninsu.

Tsohon shugaban kasar yayinda ya ke bayyana tattaunawa da wasu shugabannin Afrika a kwanan nan, ya ce sauran kasashen nahiyar na kallon Najeriya a matsayin wani babban yaya, amma su kan nuna ramuwar cewa ba a magance lamarin hadin kai da tsaro ba.

Ya zama dole mu yi aiki da addu’a don Najeriya ta inganta, In ji Obasanjo
Ya zama dole mu yi aiki da addu’a don Najeriya ta inganta, In ji Obasanjo
Asali: Twitter

Jakadan wanda ya samu jagorancin Bishop Precious Amuku ya kawo sakon zaman lafiya zuwa ga tsohon shugaban kasar a gabannin zagayowar ranar haihuwarsa karo na 83.

KU KARANTA KUMA: Babban magana: Za a gurfanar da gwamnan Taraba a gaban kotu

An yi wa tsohon shugaban kasar addu’o’in tsawon rai, zaman lafiya a Najeriya, Afrika da duniya baki daya.

A bangare daya mun ji a baya cewa Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya ce Najeriya na bukatar sabon kundun tsarin mulki don ci gaban kasar nan.

Ya sanar da hakan ne a taron farko na tunawa da Dr. Fredrick Fasehun, wanda ya kirkiro kungiyar jama’ar Odua (OPC) a jihar Legas.

Tsohon shugaban kasar ya kara da cewa Najeriya dole ne ta damu da gyaran kasar nan don kawo ci gaba. Obasanjo ya jaddada cewa akwai bukatar gyara a duk fadin kasar nan.

Kamar yadda ya ce, karuwar rashin tsaro a kasar nan ta assasa abubuwa da yawa da ke faruwa a kasar nan. Yace gwamnoni a matsayinsu na shugabannin tsaron jiharsu ba zasu iya yin shiru a bangaren garkuwa da mutane, daba da kuma ta’addancin Boko Haram.

Obasanjo ya dau alkawarin ci gaba da tabbatar da hadin kan kasar nan har zuwa mutuwarsa. Ya jajanta rashin yarda da ke tsakanin kungiyoyi da yankunan kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel