Gwamna El-Rufai ya yi alkawarin kawo karshen kashe-kashen mutane a Jihar Kaduna

Gwamna El-Rufai ya yi alkawarin kawo karshen kashe-kashen mutane a Jihar Kaduna

Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa ba zai yi wa ‘Yan bindiga lamuni ko kuma ya zauna da su domin ayi wani sulhu ba.

Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa gwamnatinsa ba za ta sasanta da ‘Yan bindiga ba ne a lokacin da ya ziyarci Kauyukan da aka kashe mutane a jihar.

Nasir El-Rufai ya kuma ba mutanen da ya ke shugabanta hakuri a game da gazawar da ya yi wajen kare rayukansu. Hakan na zuwa ne bayan an kai hare-hare a Igabi.

Tawagar gwamnan ta kai ziyara zuwa Karewa da wasu Kauyuka da ke cikin karamar hukumar Igabi da Giwa inda aka hallaka sama da mutane 51 a Ranar Lahadi.

“Na zo ne in ba ku hakuri a game da gazawar da mu ka yi na kare ku kamar yadda ya kamata, mu na bakin kokarinmu na rage aukuwar wannan.” Inji Malam El-Rufai.

KU KARANTA: Gwamnan Kaduna zai sa kafar wando daya da masu kashe mutanensa

Gwamna El-Rufai ya yi alkawarin kawo karshen kashe-kashen mutane a Jihar Kaduna
Gwamna Nasir El-Rufai ya sha alwashin kare mutanen Jihar Kaduna
Asali: Facebook

“Ba don agajin gaggawar da Jami’an tsaro su ka kawo ba, da an ruguza duk Kauyukan nan.” Gwamnan ya kuma roki Jama’an Yankin su cigaba da yi masa hakuri.

“Mu na kokarin ganin mun kawo karshen wannan matsala domin Jami’an tsaro su na kan aiki. A Kaduna mu na da yalwar fili. Idan an toshe nan, sai a kai hari a can.”

Gwamnan ya yaba da irin kokarin da Jami’an sojin sama da na kasa da kuma irin rawar da DSS da ‘Yan Sanda su ka taka na ganin an takaita harun da ake kai wa.

El-Rufai ya yi addu’a ga wadanda su ka rasu tare da bada umarni ga hukumar SEMA mai bada agajin gaggawa a jihar ta dauki nauyin wadanda aka yi wa ta’adi.

Daily Trust ta ce wadanda su ka yi wa gwamnan rakiya sun hada da Darektan DSS, GOC I, Kwamishinan ‘Yan Sanda, shuganannin kananan hukumomi da Hakimai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel