PDP ta yi nasara a zaben Kansilolin kananan hukumomi a Jihar Enugu

PDP ta yi nasara a zaben Kansilolin kananan hukumomi a Jihar Enugu

Mun samu labari daga Jaridar nan ta Daily Trust cewa jam’iyyar PDP ta samu gagarumar nasara a zabukan da aka shirya a jihar Enugu a karshen makon da ya wuce.

Jaridar ta bayyana cewa PDP ce ta samu nasara a zaben Kansilolin Mazabun da aka shirya a kananan hukumomin da ke Enugu kamar yadda hukumar zabe ta sanar.

Shugaban hukumar zaben jihar Enugu, ENSIEC, Dr. Mike Ajogwu, ya tabbatar da cewa ‘Yan takarar jam’iyyar PDP ne su ka lashe zaben da aka gudanar a Ranar Asabar dinnan.

“A zaben ke-ke-da-ke-ken da ba a taba yin irinsa a jihar Enugu ba, ‘Yan takarar jam’iyyar PDP da su ka shiga zaben kananan hukumomin 2020, sun doke sauran jam’iyyu.”

Mike Ajogwu ya sanar da sakamakon wannan zabe ne a jiya Ranar Lahadi. Ajogwu ya ce PDP ta yi galaba a kan sauran jam’iyyun siyasa 35 da su ka shiga wannan takara.

KU KARANTA: Manyan Jam’iyyar hamayya sun koma APC a Jihar Ondo

PDP ta yi nasara a zaben Kansilolin kananan hukumomi a Jihar Enugu
Ugwuanyi ya kai PDP ga nasara a kananan zabuka a Jihar Enugu
Asali: UGC

Shugaban hukumar ENSIEC ya fitar da sakamakon zaben gaba daya Kansilolin da ke cikin kananan hukumomi 17 na jihar. Babu jam’iyyar da ta iya samun wata kujera.

Daya daga cikin sababbin shugabannnin kananan hukumomin jihar, Solomon Onah wanda ya lashe zabe a karamar hukumar Udenu kwanaki, ya ce PDP ta karbe kaf Enugu.

Mista Onah ya bayyana cewa irin salon mulkin Mai girma gwamna Ifeanyi Ugwuanyi na jam’iyyar PDP ne ya ba su damar samun wannan nasara da ta mamaye jihar.

Idan ba ku manta ba, a zaben kananan hukumomi, haka PDP ta samu irin wannan nasara. PDP za kuma ta samu kujeru 260 na Kansilolin jihar kamar yadda Onah ya bayyana.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel