Yan watanni da barin Majalisa: Dino Melaye ya fara kukan dawainiya sun masa yawa

Yan watanni da barin Majalisa: Dino Melaye ya fara kukan dawainiya sun masa yawa

- Dino Melaye ya ce dawainiyar da ya ke kansa sun fara nauyi sannan ya yi kira ga Allah da ya Kara masa falala da nasara

- Korafin tsohon dan majalisar mai ban dariya na zuwa ne kasa da shekara daya bayan ya rasa kujerarsa na Majalisar dattawa inda abokin adawarsa Smart Adeyemi ya dare

- Melaye ya wakilci yankin Kogi ta Yamma a Majalisar dattawa lokacin da Bukola Saraki ke wakiltan Majalisar ta takwas kafin ya sha kaye a yunkurinsa na neman zarcewa

Ga dukkan alami Dino Melaye, wani tsohon sanata mai wakiltan Kogi ta yamma ya fara fuskantar abubuwa kamar kowa bayan tsohon dan majalisar ya je shafin zumunta don yin korafi a kan abun da ya yi wa lakabi da “nauyin bukatu”.

Melaye ya yi aiki a matsayin sanata a majalisar dattawa ta takwas amma dawowarsa majalisa ta hadu da cikas bayan kaye da ya sha a hannun Smart Adeyemi a zaben da aka sake a yankin Kogi ta yamma.

Tsohon sanatan mai shekara 46, wanda kwanan nan ya mallaki wani katafaran gida, a yanzu yana korafi a kan nauyin bukatunsa da ya ce sun karu, inda dama halinsa me yin barkwanci.

A wani bidiyo mai tsawon sakwan 52 da ya wallafa a shafinsa na Twitter, tsohon dan majalisar ya ce yana bukatar “karin falala da nasara” Yayinda “nauyin bukatunsa ke karuwa.”

KU KARANTA KUMA: Badakalar layin wayar Hanan Buhari Umarni daga fadar shugaban kasa ne ya sa muka tsare mutumin tsawon makonni ba tare da gurfanar dashi ba – SSS

“Allah Ina neman karin falala da nasara,” cewar Melaye a ranar Litinin, 2 ga watan Maris. “Nauyin dawainiyana na karuwa. Ka kara tallafa mun ya Ubangiji.”

Tsohon dan majalisar ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook amma daga bisani ya goge shi biyo bayan sharhin da aka ta yi kan bidiyon.

A wani labari na daban, mun ji cewa Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya ce matatar Dangote za ta dibi yan Najeriya sama da 70,000 aiki idan ta fara aiki.

Ya ce manufofi daban daban da gwamnatin tarayya ta tanadar zai rage yawan rashin aikin yi a kasar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel