Matatar Dangote za ta kwashi ma’aikata sama da 70,000, in ji bankin CBN

Matatar Dangote za ta kwashi ma’aikata sama da 70,000, in ji bankin CBN

- Godwin Emefiele, wamnana babban bankin Najeriya ya ce matatar Dangote za ta dibi yan Najeriya sama da 70,000 aiki idan ta fara aiki

- Emefiele ya ce manufofi daban daban da gwamnatin tarayya ta tanadar zai rage yawan rashin aikin yi a kasar

- Shugaban gidauniyar Dangote, Alhaji Aliko Dangote ma ya ce yana wani aiki na rage yawan marasa aikin yi a kasar

Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele ya ce matatar Dangote za ta dibi yan Najeriya sama da 70,000 aiki idan ta fara aiki.

Ya ce manufofi daban daban da gwamnatin tarayya ta tanadar zai rage yawan rashin aikin yi a kasar.

Gwamnan babban bankin wanda ya yi jawabi ga manema labarai bayan gama zagaye matatar a karshen mako, ya ce ana sanya ran cewa matatar Dangote zai habbaka ma’aikatansa daga yanda suke a yanzu 34,000 zuwa 70,000 lokacin da zai fara aiki.

Matatar Dangote za ta kwashi ma’aikata sama da 70,000, in ji bankin CBN
Matatar Dangote za ta kwashi ma’aikata sama da 70,000, in ji bankin CBN
Asali: Facebook

Har ila yau, Shugaban gidauniyar Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya ce yana wani aiki na rage yawan marasa aikin yi a kasar.

Ya ce shukan zai dawo da musayar ciniki da kasashen waje yayinda Najeriya ta zama mai dogaro da kai a matatar man fetur.

A cewarsa, kamfanin takin shuka na dala biliyan 2 a Ibeju-Lekki a jahar Lagas zai fara aiki a watan Mayu.

Shahararren dan kasuwan ya ce kamfanin takin zai sa Najeriya ta zama ita kadai ce kasar da ke fitar da takin a yakin Afrika ta Sahara sannan zamo mafi girma wacce ka iya samar dad ala biliyan 2.5 duk shekara.

Danote ya ce an fara gwada tin, inda ya kara da cewa aikin zai zamo mafi girma a duniya da karfinta na samar da tan miliyan 3 duk shekara.

KU KARANTA KUMA: Badakalar layin wayar Hanan Buhari Umarni daga fadar shugaban kasa ne ya sa muka tsare mutumin tsawon makonni ba tare da gurfanar dashi ba – SSS

A cewarsa, matatar wacce ta kai kaso 48 cikin 100 wajen kammaluwa za ta sanya Najeriya zama mafi girma wajen fitar da kayayyakin fetur a Afrika.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel