Gwamna Ganduje ya yi daidai da ya haramta bara a Kano sai dai kuma … – Inji KCCI

Gwamna Ganduje ya yi daidai da ya haramta bara a Kano sai dai kuma … – Inji KCCI

Wasu Dattawan jihar Kano a karkashin inuwar kungiyar “Kano Concerned Citizen Initiative” ta KCCI ta yabawa matakin da gwamnati ta dauka na hana bara a fadin jihar.

Wannan kungiya ta Dattawan da su ka damu da jihar Kano sun ce tsarin da Mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya kawo na haramta bara zai taimaki jihar Kano.

Sai dai duk da ganin kokarin Dr. Ganduje, wannan kungiya ta soki gwamnan a dalilin daukar wannan mataki da ya yi ba tare da ya tuntubi masu ruwa da tsaki a harkar ba.

Kungiyar ta yi wannan bayani ne ta bakin shugaban ta watau Alhaji Bashir Othman Tofa a wajen wani babban taro da ta shirya a game da harkar Almajiranci da bara a Kano.

“Ganin yadda ake da miliyoyin Almajirai su na gantali a hanya, wasunsu sun koma bara domin samun abinci, saka su a makarantar boko ya na bukatar hangen nesa.”

KU KARANTA: Ministan Najeriya Sheikh Pantami ya na tare da Ganduje a kan hana bara

Gwamna Ganduje ya yi daidai da ya haramta bara a Kano sai dai kuma … – Inji KCCI
Tofa ya ce ya kamata ace Ganduje ya tuntubi jama'a kafin ya hana bara
Asali: Twitter

Bashir Othman Tofa ya nuna cewa, haramta bara a Kano ba tare da kawo wasu hanyoyi da za su tabbatar da wannan shiri da aka yi ba, zai kawowa matakin matsala a karshe.

A na sa ra’ayin, shugaban KCCI, Tofa ya na ganin cewa ya kamata ace gwamna Abdullahi Ganduje ya tuntunbi wadanda ke da ta cewa a harkar bara kafin ya fito da tsarin.

“Babu shakka mu na goyon-bayan gwamnati na haramta bara a kan hanya domin hakan daidai ne ga jihar Kano. Amma mu na ganin akwai bukatar a zauna da jama’a.”

Haka zalika Alhaji Tofa yaba da yunkurin da ake yi na kawo garambawul a tsarin Tsangaya, inda ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano ta tashi tsaye wajen cin ma wannan buri.

Yahuza Getso wanda ya na cikin ‘Yan kungiyar KCCI, ya yi kira ga gwamnatin Ganduje ta tuntubi Malaman da ke jihar Kano domin samun adadin Almajiran da ake da su.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel