Labari da dumi-dumi: Pa Kasunmu Kayode Odumosu ya mutu

Labari da dumi-dumi: Pa Kasunmu Kayode Odumosu ya mutu

Labari ya na zuwa mana cewa tsohon ‘Dan wasan kwaikwayon nan Kayode Odumosu, wanda aka fi sani da Pa Kashumu ya riga mu gidan gaskiya.

A halin yanzu an fara makoki a gidan wasan kwaikwayon Nollywood a sakamakon mutuwar ‘Dan wasa Kayode Odumosu wanda ya yi fama da jinya.

Taurariyar ‘Yar wasa Foluke Daramola-Salako ce ta sanar da mutuwar wannan Dattijon ‘Dan wasa a shafinta na sada zumunta na Instagram dazu nan.

Foluke Daramola-Salako ta bayyana cewa mutuwar wannan Dattijo wanda ta kira kwararren ‘Dan wasan kwaikwayo abin koyi, ya yi wa jama’a ciwo

Kamar yadda ku ka sani, tun kwanakin baya aka ji labari cewa Bayaraben ‘Dan wasan kwaikwayon mai shekaru 66 a Duniya bai da lafiya.

KU KARANTA: 'Yan siyasan da su ka mutu a sanadiyyar hadarin mota

A yau, Lahadi, 1 ga Watan Maris 2020, Kayode Odumosu ya ce ga garinku nan. Sai dai ba mu da labarin takamaimen lokacin da ‘Dan wasan ya cika ba.

Kafin yanzu Legit.ng ta rahoto cewa Pa Kasunmu ya makance, sannan kuma ta kai bai ita tafiya. ‘Dan wasan bai iya samun kudin zuwa asibitin waje ba.

Zuciyar Marigayin da hantarsa duk sun samu matsala wanda a dalilin haka, su ka yi sanadiyyar rashin ganin da kuma jawo masa yawan mantuwa.

A watan da ya wuce ne Frank Dallas Ebulukwu wanda shi ma shararren ‘Dan wasan fim ne ya rasu. Dallas Ebulukwu ya rasu ne wajen wani taro a Abia.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel