Siyasar Zamfara: Wani kwamishina ya bukaci Gwamna Matawalle da ya koma APC

Siyasar Zamfara: Wani kwamishina ya bukaci Gwamna Matawalle da ya koma APC

- Wani kwamishinan gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara ya bukace shi da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC)

- Alhaji Abubakar Abdullahi Tsafe, kwamishinan ci gaban karkara da ma’aikatu, ya ce sauya shekar gwamnan zai karfafa tarin nasarorin da aka samu a jahar

- Kwamishinan ya kasance daya daga cikin masu ruwa da tsaki na APC da Matawalle ya ba mukami a gwamnatinsa

Daya daga kwamishinonin gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara ya bukace shi da ya sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Kotun koli ce ta kaddamar da Matawalle wanda ya kasance dan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin Gwamna bayan APC a jahar Zamfara ta ki gudanar da zaben fidda gwani a lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta bata.

Alhaji Abubakar Abdullahi Tsafe, kwamishinan ci gaban karkara da ma’aikatu, ya ce sauya shekar gwamnan zai karfafa tarin nasarorin da aka samu a jahar.

Siyasar Zamfara: Wani kwamishina ya bukaci Gwamna Matawalle da ya koma APC
Siyasar Zamfara: Wani kwamishina ya bukaci Gwamna Matawalle da ya koma APC
Asali: UGC

Kwamishinan ya yi sanarwar ne yayinda ya ke jawabi ga magoya bayan APC a karamar hukumar Tsafe a ranar Asabar, 29 ga watan Maris.

KU KARANTA KUMA: Babu abun da wani ya isa ya yi idan na nada dana shugaban ma’aikata - Akeredolu

Kwamishinan ya kasance daya daga cikin masu ruwa da tsaki na APC da Matawalle ya ba mukami a kokarin gwamnan na tafiya da kowa a gwamnatinsa.

Ya bukaci Gwamna Matawalle da ya koma APC don kai jahar zuwa mataki na gaba.

A wani labari na daban, mun ji cewa an tsare wasu 'yan jam'iyyar PDP biyu a gidan yari bayan an gurfanar da su a gaban kotu bisa zarginsu da zagin gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya.

Garkame 'yan jam'iyyar dawar ya saka jihar Gombe a cikin jern jihohin da a kwanakin baya bayan nan suka daure masu sukar gwamnoninsu.

Jaridar Premium Times ta wallafa wani rahoto da ke nuna yadda gwamnonin a fadin Najeriya ke cigaba da farautar masu sukansu a dandalin sada zumunta bisa hujjar cewa suna zaginsu.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel