Zargin zagin gwamnan APC: An tsare Atiku Boza na PDP a kurkuku, an garkame wanda ya je belinsa

Zargin zagin gwamnan APC: An tsare Atiku Boza na PDP a kurkuku, an garkame wanda ya je belinsa

An tsare wasu 'yan jam'iyyar PDP biyu a gidan yari bayan an gurfanar da su a gaban kotu bisa zarginsu da zagin gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya.

Garkame 'yan jam'iyyar dawar ya saka jihar Gombe a cikin jern jihohin da a kwanakin baya bayan nan suka daure masu sukar gwamnoninsu.

Jaridar Premium Times ta wallafa wani rahoto da ke nuna yadda gwamnonin a fadin Najeriya ke cigaba da farautar masu sukansu a dandalin sada zumunta bisa hujjar cewa suna zaginsu.

An tura Atiku Boza-Boza da Adamu Babale gidan yari bisa umarnin wata kotun jihar Gombe bayan an gurfanar da su da zargin hada kai tare da niyyar zagi da cin mutunci, kamar yadda takardar tuhumarsu da Premium Time ta gani ta bayyana.

A ranar Laraba ne aka tsare Boza-Boza a ofishin rundunar 'yan sanda reshen Pantami a cikin garin Gombe bayan an shigar da korafi a kansa. Sai dai, rundunar 'yan sanda bata bayyana wanda ya shigar da korafin ba.

Zagin gwamnan APC: An tsare Atiku Boza na PDP a kurkuku, an garkame wanda ya je belinsa
Atiku Boza da Adamu Babale
Asali: Twitter

Boza-Boza tsohon hadimi ne ga tsohon gwamnan jihar Gombe a karkashin inuwar jam'iyyar PDP, Ibrahim Dankwambo.

An sake garkame Adamu Babale, na hannun damar Boza-Boza, bayan ya je ofishin 'yan sanda domin neman belinsa a matsayinsa na dan jam'iyyar PDP.

A ranar Alhamis ne aka gurfanar da Boza-Boza da Babale, daure da ankwa, a gaban kotu da ke Pantami bisa tuhumarsu da hada baki domin zagin gwamna Yahaya.

A cewar takardar shigar da kara da 'yan sanda suka gabatar a gaban kotun (FIR), an zargi 'yan jam'iyyar adawar biyu da kiran gwamna Yahaya da "shugaban masu karya alkawari.

Zagin gwamnan APC: An tsare Atiku Boza na PDP a kurkuku, an garkame wanda ya je belinsa
Atiku Boza da Adamu Babale
Asali: Twitter

Takardar karar ta bayyana cewa laifin 'yan adawar ya saba da sashe na 96 da na 155 na kundin dokokin aikata laifuka da hukuncinsu (Penal Code).

An gurfanar da su ne a gaban kotu ranar Alhamis, ranar da dukkan kotunan jihar ke yin hutu, kamar yadda sanarwa daga ofishin alkalin alkalan jihar, Muzau Pindiga, ta nuna.

DUBA WANNAN: Tsoho mai shekaru fiye da 100 ya auri budurwa 'yar 20 (Hotuna)

Amma hakan bai hana kotu sauraron karar da aka shigar ba tare da bayar da umarnin a tsare su a gidan yari ba, lamarin da jam'iyyar PDP ta bayyana cewa wata kullalliya ce aka shirya domin cin mutuncin mambobinta.

Da yake magana ta wayar tarho da Premium Times da safiyar ranar Lahadi, Abdullahi Misilli, kakakin gwamna Yahaya, ya bayyana cewa babu hannun gwamna a cikin halin da 'yan adawar suka fada.

"Ba gaskiya bane. Gwamna bai bayar da umarnin kama kowa ba. Idan ma sun samu matsala da wasu mutanen, gwamna bashi da masaniya, babu hannunsa a ciki," a cewar Misilli.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel