Rufe iyakoki: Abin da ya fi dacewa ayi kenan a yanzu – Inji Aliko Dangote

Rufe iyakoki: Abin da ya fi dacewa ayi kenan a yanzu – Inji Aliko Dangote

Shugaban kamfanin nan na Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya nuna cikakken goyon bayansa ga tsarin gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari na rufe iyakokin Najeriya.

Aliko Dangote ya nuna cewa matakin da shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya dauka na rufe iyakokin kasar ya yi masa daidai a halin da kasar ta ke ciki a yanzu.

Attajirin ya kuma musanya rade-radin da ake yi na cewa rufe iyakokin kasan Najeriya ya na cikin abubuwan da su ka jawo ribar kamfanin simintinsa ya yi kasa a shekarar 2019.

Dangote ya ce rufe iyakokin kasan Najeriya shi ne abin da ya fi dacewa da tattalin arzikin kasar a halin yanzu, ya kuma ce babu yadda za ayi ace hakan ya karya kamfunansa.

Mai kudin Afrikan ya bayyana cewa ya na ta bunkasa kamfunan simintinsa na Dangote a kasashen Afrika, don haka garkame iyakokin Najeriya ba zai yi tasiri a kansa ba.

KU KARANTA: Matatar Dangote da za ta rike tace gangunan mai 650, 000 za ta fara aiki

Rufe iyakoki: Abin da ya fi dacewa ayi kenan a yanzu – Inji Aliko Dangote
Duk da kalubalen Afrika, Dangote ya na samun ribar kasuwanci a Afrika
Asali: UGC

Attajirin ya yi wannan jawabi ne a Ranar Alhamis da ta gabata, ya na mai tabbatar da cewa kamfunan simintinsa su na samun metric ton 9.6 na siminti a kasashen Afrika.

A jawabin ‘Dan kasuwar ta bakin wani babban Ma’aikacinsa, Joe Makoju, kamfanin simintin ya na cigaba da mamaye sauran kamfanoni a kasuwar hannun jarin Najeriya.

“Kamfanin simintin Dangote da ke Mtwara, kasar Tanzaniya, ya samu karin 94% na buhunan simintin da ake fitarwa. Kamfanin Sanagal ya samu karin ciniki da 100%.”

“Adadin simintin da Dangote ya saida a 2019 ya doshi metric ton 9.6 daga metric tan 9.4.” Kamfanin kuma ya amince da N16 a matsayin kudin hannun jari. Inji Makoju.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel