'Yan daba sun hargitsa taron wayar da kai na dan majalisar tarayya

'Yan daba sun hargitsa taron wayar da kai na dan majalisar tarayya

A ranar Juma'a ne 'yan daba suka hargitsa taron wayar da kai a kan shaye-shaye da ta'ammalli da miyagu kwayoyi da dan majalisar tarayya, Julius Ihonvbere ya shirya a kwalejin Michael Imoudu da ke Auze, karamar hukumar Owan ta gabasa a jihar Edo.

'Yan daban sun kutsa wajen taron ne inda suka kora mashirya shirin da kuma wadanda suka halarta.

Wasu daga cikinsu kuwa sun samu raunika yayin da suke kokarin barin wajen taron.

Ihonvbere dai na hannun daman shugaban jam'iyyar APC na kasa ne, Adams Oshiomhole, kuma ana zargin wasu 'yan siyasa na hannun daman Gwamna Godwin Obaseki ne suka dau nauyin wannan harin.

Shugaban karamar hukumar Owan ta gabas, Andy Osigwe, wanda aka zarga a matsayin mashiryin harin, ya sanar da manema labarai cewa ba 'yan daba bane suka watsa taron, jami'an tsaro ne.

Ya ce shi ya bada umarnin katse taron don ba a sanar da karamar hukumar ba.

Osigwe ya ce, "Na umarci jami'an tsaro ne da su dakatar da taron kuma su rufe wajen, amma ba 'yan daba ba."

'Yan daba sun hargitsa taron wayar da kai na dan majalisar tarayya
'Yan daba sun hargitsa taron wayar da kai na dan majalisar tarayya
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Wata sabuwa: Mata yanzu suna tafasa audugar mata suna shan ruwan don maye - NDLEA

A yayin zantawa da manema labarai, hadimin Ihonvbere mai suna Ekundayo Bright ya ce, "Abin bai yi dadi ba ta yadda Owan ta zama karamar hukumar da ta tara 'yan daba da 'yan ta'adda."

A wani labari na daban, dakarun sojojin Najeriya sun kama wata da ake zargin 'yan bindiga ce, Zainab Abubakar, a Unguwan Salaha, Mararaban Jos a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Rundunar sojin ta ce a ranar Alhamis cewa binciken da aka fara gudanarwa a wayar salular wace ake zargi 'ya nuna ta tana tika rawa rataye da bindiga AK - 47 a wuyan ta.'

The Punch ta ruwaito cewa Dakarun sojojin 1 Division Garrison a karkashin Operation Mesa ta kama Zainab Abubakar ne a ranar Litini.

Mai kula da sashin yada labarai na rundunar sojin Najeriya, Kwanel Aminu Iliyasu, ya tabbatar wa manema labarai kama wacce ake zargin inda ya ce, "Dakarun 1 Division Garrison ta kama wata 'yar bindiga mace a Unguwan Salaha a Mararaban Jos. Binciken da aka gudananar da fari ya nuna bidiyo a cikin wayar ta tana tika rawa da bindiga AK-47 a wuyan ta wurin wani taro."

"Dakarun sojojin ta suka kai sintiri a kusa da kauyen Kirsa a karamar hukumar Anka a jihar Zamfara sun tare wani mai babur da ke dauke da wata budurwa. Sai dai mai tuka babur din ya saki babur din sannan budurwar ta tsere ta shiga daji. Bayan hakan sojojin sun kama budurwar, sun kwato AK-47 guda daya daga hannun ta, wani AK-47 din da harsashi guda 30 masu tsawon 7.65mm da kuma babur kirar Honda." Ya kara da cewa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel