Asiri ya tonu: An kama tsohon sojan sama yana shugabantar wasu takadiran 'yan fashi

Asiri ya tonu: An kama tsohon sojan sama yana shugabantar wasu takadiran 'yan fashi

- Wani tsohon jami’in rundunar sojin Najeriya da aka kora ya shiga hannun jami’an tsaro

- Runduna ta musamman da ke farautar ‘yan fashi ce ta kamo shi tare da wasu mutane hudu da suke wa fasinjoji fashi

- Kamar yadda ya bayyana, abokin shi da ke kasar Jamus ne ya aiko mishi da motar wacce ya koma fashi ga fasinjoji da ita

Wanda ake zargin, Matthew Tokeme mai shekaru 50 ya shiga hannun ‘yan sanda a ranar Talata. An kama tsohon ma’aikacin a rundunar sojin saman Najeriya din tare da motar shi kirar Sienna wacce yake amfani da ita don fashi.

Wata takardar da RRS ta fitar, ta ce Tokeme ya shiga hannunsu ne tare da wasu mutane hudu na kungiyar bayan sun gama aiki a Ojodu kan hanyar Abule da ke Iyana-Ipaja a Ikeja tsakanin karfe 5 zuwa 6 na safe.

Sunyi wa fasinjoji fashi ne wadanda suka hada da mata. Wadanda ake zargin tare da sauran ‘yan kungiyar suna aiki ne da sunayen da suka hada da Papa, Brown, Oyeewo da Segun.

Tokeme ne mamallakin motar mai kirar Sienna da lamba APP 488 FH. ‘Yan sandan sun bayyana cewa motar mai launin bula ta shigo hannun shi ne bayan da wani abokinshi da ke kasar Jamus ya aiko mishi da ita.

Bayan rundunar ‘yan fashin sun kwacewa fasinjojin kudinsu, sai suka ajiyesu a wani waje da sassafe, cewar takardar.

KU KARANTA: A karon farko an samu wani kare da cutar Coronavirus a birnin Hong Kong

Daya daga cikin wadanda suka yi wa fashin ya sanar da Kwamandan RRS din, DCP Olatunji Disu a kan ayyukan rundunar ‘yan fashin. A take kuwa ya tura rundunar ‘yan sandan don damko ‘yan fashin.

Wanda aka yi wa fashin ya bayyana cewa sun kwace mishi na’ura mai kwakwalwa da kudadenshi.

A lokacin da aka tuhumi wanda ake zagin, ya amsa laifin shi. “Abokina da ke kasar Jamus ne ya turo min motar don in dinga amfani da ita don samun kudi. Ya siya min motar ne bayan ya gano cewa kasuwanci na baya tafiya dai-dai. Amma kuma sai na fara amfani da motar wajen kwacewa fasinjoji kudi da kadarorin da sassafe.” Ya ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel