Yanzu Yanzu: An gano mutanen da suka yi hulda da dan kasar Italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus

Yanzu Yanzu: An gano mutanen da suka yi hulda da dan kasar Italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus

- Kamfanin simintin da ke jahar Ogun, Lafarge Africa Plc ta tabbatar da cewar mutum na farko da aka samu yana dauke da cutar Coronavirus a Najeriya ya ziyarce ta a Ekwekoro, jahar Ogun

- Folashade Ambrose-Medebem, kakakin kamfanin, ta bayyana hakan a wani jawabi a ranar Juma’a

- Ta ce sun gano dukkanin wadanda suka suka yi hulda da mutumin

Lafarge Africa Plc, wata kamfanin siminti ta tabbatar da cewar dan kasar Italiyan da ya kasance mutum na farko da aka samu yana dauke da cutar Coronavirus a Najeriya ya ziyarce ta a Ekwekoro, jahar Ogun.

Folashade Ambrose-Medebem, kakakin kamfanin, ta bayyana hakan a wani jawabi a ranar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu.

Ta ce an gano dukkanin wadanda suka yi hulda da dan kasar Italiyan wanda ba a bayyana kowanene ba.

Yanzu Yanzu: An gano mutanen da suka yi hulda da dan kasar Italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus
Yanzu Yanzu: An gano mutanen da suka yi hulda da dan kasar Italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus
Asali: Facebook

“Gwamnatin jahar Lagas ta kawo rahoton lamarin Coronavirus na farko a Najeriya. Mutumin da ake magana a kai ba yiwa wani dan kasuwa da ke abokin kasuwancin Lafarge Africa plc a jahar Ogun aiki,” in ji sanarwar.

“A matsayinmu na masu kasuwanci, mun yi gaggawan gano mutanen da suka yi hulda da mutumin kai tsaye. Mun kuma shirya kebance su.

“Muna godiya ga irin jagoranci na ma’aikatar lafiya ta tarayya, gwamnatocin jihohin Lagas da Ogun da kuma hukumomin gwaje-gwaje kuma muna ba hukumomin cikakken hadin kai."

KU KARANTA KUMA: Newcastle ta hana musafaha saboda cutar coronavirus

A halin da ake ciki, mun ji cewa Gwamnatin jihar Ogun ta sanar da cewa an kulle kamfanin Simintin Larfarge dake Ewekoro a jihar bayan tabbatar da shigar mutumin da ya kwaso Coronavirus Najeriya harabar kamfanin.

Gwamnatin jihar ta ce, dan kasar Italiyan, wanda yake aiki da kamfanin Larfarge Africa ya ziyarci kamfanin Simintin ranar Talata.

Kwamishnar kiwon lafiyan jihar, Dakta Tomi Coker, wacce ta bayyana hakan ranar Juma'a yayin hira da manema labarai a Abekuta, babbar birnin jihar, ta ce ya fara zazzabi ne kuma aka fara jinyarsa a asibitin dake cikin kamfanin Lafarge kafin komawarsa Legas ranar Laraba.

Kwamishanar, tare da kakakin gwamnan jihar, Remmy Hazzan, da manyan ma'aikatan ma'aikatar sunce masana kwayoyin cuta sun fara tattara dukkan wadanda ya hadu da su a lokacin da je jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel