Newcastle ta hana musafaha saboda cutar coronavirus

Newcastle ta hana musafaha saboda cutar coronavirus

Kungiyar kwallon kafa ta Newcastle ta haramta yin musafaha a tsakanin yan wasanta a kokarin da ta ke yi na hana yaduwar cutar Coronavirus, shugaban kungiyar Steve Bruce ya bayyana a ranar Juma’a, 28 ga watan Fabrairu.

“Muna da wata al’ada na yin musafaha a duk lokacin da muka hadu da abokanmu da safe - mun dakatar da hakan bisa ga shawarar likitoci.

“Mun kasance kamar sauran jama’a, muna gaban talbijin don ganin inda cutar za ta je a nan gaba muna kuma fatan ba za ta munana ba a wannan kasar," in ji Bruce

Newcastle ta hana musabaha saboda cutar coronavirus
Newcastle ta hana musabaha saboda cutar coronavirus
Asali: UGC

An soke wasanni da dama, ciki har da Six Nations rugby da Chinese Grand Prix, saboda cutar ta coronavirus, wacce ta samo asali daga kasar China amma tuni ta watsu zuwa kasashe fiye da guda 50.

Newcastle ta ce tana bin shawarwarin da hukumomin lafiya da gwamnatin Birtaniya suka bayar ne kan yadda za a kauce wa makuwa da cutar.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Dan Italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus ya ziyarci Ogun

Ita ma Arsenal ta bullo da wasu karin matakai a kan 'yan jaridar da za su halarci taron manema labaranta ranar Asabar a filin wasanta, yayin da Everton ta tuntubi ma'aikatanta inda ta gaya musumatakan da gwamnatin ta fito da su don kauce wa kamuwa da cutar.

Kungiyar Valencia ta soke "dukkan taruka a rufaffen wuri wanda wanda ka iya zama barazana ga 'yan wasa da koci-koci da kuma ma'aikata" bayan an tabbatar da barkewar coronavirus a birnin.

A wani labari makamancin haka mun kawo muku rahoton cewa Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya tabbatar da bullar cutar Coronavirus mai kisa a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma'ar nan 28 ga watan Fabrairu.

A yadda sanarwar ta nuna, cutar ta shafi wani dan kasar Italiya ne wanda yake aiki a Najeriya, wanda ya dawo daga birnin Milan ya shigo Legas a ranar 25 ga watan Fabrairu.

An tabbatar da cutar a jikinshi, bayan gabatar da gwaje-gwaje a babban asibitin koyarwa na jami'ar Legas, a fannin binciken cututtuka. Ma'aikatar lafiyan ta tabbatar da cewa, mutumin yana nan yana karbar magani, kuma yana samun sauki a hankali a hankali.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel