Na dauki wani dan Italiya a mota daga filin jirgin sama ranar Laraba - Wani direba ya fito

Na dauki wani dan Italiya a mota daga filin jirgin sama ranar Laraba - Wani direba ya fito

- Cutar CoronaVirus ta bulla a jihar Legas, Najeriya

-Wani dan Najeriya ya bayyanawa duniya a shafin Tuwita cewa shine direban da ya dauki mutumin kasar Italiyan da ya shigo da cutar daga filin jirgin sama

- Yan Najeriya sun yaba masa da wannan abu da yayi

Yan Najeriya sun waye gari da labarin cewa cutar Coronavirus ta bulla a Najeriya, kimanin wata daya da bullar a kasashen duniya 50.

Ba tare da bata lokaci ba, Gwamnatin jihar Legas ta ce jamianta sun bazama neman dukkan wadanda dan kasar Italiyan da ya kawo cutar Najeriya ya hadu da su tun ranar da ya shigo.

Bayan wannan sanarwa, wani matashin Najeriya mai suna Olugbega Bodunrin(@boldjohnson07), ya fito shafinsa na Tuwita inda ya bayyana cewa shi ya dauki wani dan kasar Italiya daga filin jirgin saman Murtala Mohammed shekaran jiya.

A cewarsa, Bodunrin ya bayyana cewa ya hadu da dan kasar Italiya ne ranar Laraba, 26 ga wata kuma sun yi hira tare har suka ci abinci tare.

Bodunrin ya ajiye lambar wayarsa idan akwai bukatar gwadashi.

Yayinda wasu ke yaba masa kan fitowa yayi magana, wasu sunce shima ya fara rubuta sunayen wadanda ya hadu da su tun ranar Laraba domin tuntubarsu.

Na dauki wani dan Italiya a mota daga filin jirgin sama ranar Laraba - Wani direba ya fito
Na dauki wani dan Italiya a mota daga filin jirgin sama ranar Laraba - Wani direba ya fito
Asali: Twitter

A bangare guda, Sabbin bayanai sun bayyana cewa dan italiyan da ke dauke da cutar Coronavirus ya ziyarci jahar Ogun kafin a kai shi Lagas inda aka tabbatar da cewar yana dauke da cutar.

An tattaro cewa Dan kasar Italiyan, wanda ya shigo Najeriya ta jirgin Turkiyya, ya nuna alamun cutar a jahar Ogun kafin aka yi gaggawan kais hi Lagas domin yin bincike a tsanaki a cibiyar kula da cututtuka ta Najeriya a Yaba.

Da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnati Marina, Gwamna Babajide Sanwo-Olu tare da kwamishinan lafiya na jahar, Farfesa Akin Abayomi ya bayyana cewa mutumin bai nuna kowani alama na cutar Coronavirus ba da farko.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel