Jerin manyan kasashen Turai da Coronavirus ta ratsa a Duniya
A halin yanzu cutar nan da ake gudu watau Coroavirus ta shiga kusan kowace Nahiya a Duniya. Nahiyar Antatika ce kurum ba a samu wanda ya kamu da cutar ba.
Yanzu haka wannan cuta ta shigo Najeriya, wannan na nufin Coronavirus ba ta bar Afrika a baya ba. Cutar ta fi kamari a Yankin Asiya, Amurka da kuma cikin Turai.
Mun tsakuro wasu kasashen Turai da wannan cuta ta shiga kamar yadda wtaa jarida ta bayyana:
1. Italiya
A kasar Italiya, akalla mutum 14 sun mutu a yanzu. Sama da mutane 500 sun kamu da wannan cuta.
2. Jamus
A Jamus, mutane 26 ake tunanin su na dauke da wannan cuta. Daga ciki akwai baki daga kasashen waje.
3. Faransa
A kasar Farasa an rasa mutane 2 a sakamakon wannan cuta. A dalilin haka aka hana wasu shigowa kasar.
4. Sifen
Hukumomin Sifen sun ce gano mutane 17 masu dauke da cutar. 12 daga ciki sun kamu da cutar ne a Italiya.
5. Ingila
A Birtaniya, akwai akalla mutum 12 da ke dauke da wanan cuta a yanzu. Wasu su dauko cutar ne daga Italiya.
6. Switzerland
A farkon makon nan aka tabbatar da cewa an samu wanda ya kamu da wannan cuta a kasar Switzerland.
KU KARANTA: Abubuwan da ya kamata ka sani game da cutar Coronavirus
7. Rasha
Mutanen Sin biyu ake zargin sun kamu da wannan cuta a Rasha. Kasar ta maida Bakin da aka samu da cutar.
8. Austriya
Wani Dattijo mai shekaru 72 ya kamu da cutar Coronavirus a wannan kasa. Kafinsa an samu wasu masu cutar.
9. Kuroshia
Akalla mutane uku, har da wani Matashi da ya zauna a kasar Italiya, ake zargin sun kamu da wannan cuta.
10. Girka
Hukumomi sun bada tabbacin cewa akwai Bayin Allah akalla uku da su ka kamu da wannan cuta a kasar Girka.
Sauran kasashen da ake fama da wannan cuta sun hada da:
11. Finland
12. Siwidin
13. Denmark
14. Beljika
15. Jojiya
16. Masadoniya
17. Norway da kuma kasar
18. Romaniya
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng