Da dumi-dumi: An samu bullar Coronavirus a jihar Legas
- A karon farko an samu bullar cutar coronavirus mai kisa wacce ta samo asali daga kasar China
- Cutar dai an same ta a jikin wani bature ne dan kasar Italiya, bayan yaje hutu kasarshi ya dawo jihar Legas a ranar 25 ga watan nan
- Yanzu haka dai hukumar lafiya ta tabbatar da cewa mutumin yana nan yana karbar magani, kuma za tayi iya yin ta wajen ganin cutar bata yadu a Najeriya ba
Ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire, ya tabbatar da bullar cutar Coronavirus mai kisa a wata sanarwa da ya fitar a yau Juma'ar nan 28 ga watan Fabrairu.
A yadda sanarwar ta nuna, cutar ta shafi wani dan kasar Italiya ne wanda yake aiki a Najeriya, wanda ya dawo daga birnin Milan ya shigo Legas a ranar 25 ga watan Fabrairu.
An tabbatar da cutar a jikinshi, bayan gabatar da gwaje-gwaje a babban asibitin koyarwa na jami'ar Legas, a fannin binciken cututtuka.
Ma'aikatar lafiyan ta tabbatar da cewa, mutumin yana nan yana karbar magani, kuma yana samun sauki a hankali a hankali.
Sanarwar ta kara da cewa, gwamnatin Najeriya karkashin ma'aikatar lafiya na iya bakin kokarinta wajen daukar mataki akan yaduwar cutar.
"Muna so mu tabbatarwa da 'yan Najeriya cewa mun cigaba da daura damarar yaki da wannan cuta tun lokacin da muka samu labarin bullurta a kasar China, kuma zamu yi amfani da duk wata hanya da gwamnati za ta bayar wajen ganin mun hana cutar yaduwa.
KU KARANTA: Lamari ya kai intaha: Dogarai sun yiwa Dan sanda dan karen duka saboda yaki bin dokar Sarauniya
"Mun fara gabatar da bincike domin gano mutanen da mutumin yayi mu'amala da su tun shigowar shi Najeriya. A sani cewa duk wanda ya kamu da cutar zai danyi rashin lafiya ne na dan lokaci sai ya warke, amma kuma wasu lamarin na wuce haka, musamman tsofaffi da kuma wanda suke da ciwo sosai.
"Duka 'yan Najeriya su kula da lafiyar jikinsu, su dinga yawan wanke hannayen su da kuma kula da wuraren numfashi, domin kare kai da kuma wasu daga kamuwa da cutar," cewar sanarwar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng